Za’a hukunta mahaifiyar da ta yiwa danta jina-jina a Legas

Za’a hukunta mahaifiyar da ta yiwa danta jina-jina a Legas

Za’a hukunta matar data yiwa danta mai kimanin shekara 12 mugun duka a kotu ranar Litinin, cewar daraktan hukumar kare hakkin bil adama na jihar Lagos, Biola Oseni.

Oseni yace gwamnatin jihar, ta ceto yaron wanda aka sakaye sunan a gidansu dake unguwar Agege. Al’amarin ya faru ne ranar Lahadi

Al’amarin ya yadu a Facebook, hakan yasa hukumar kare hakkin bil Adama ta dau mataki.

An ga hoton yaran a Facebook an yi masa jina-jina.

Bisa ga bayanin daraktan, yayinda ma’aikatan hukumar suka kai ziyara gidan, an bayyana musu cewa yaron yaci mugun duka ne a wurin mahaifiyarsa.

Ya kara da cewa, “Tawagar da suka ceto yaran basu samu mahaifiyar ba sai daga baya aka kamata a wani wuri daban, aka kaita ofishin yan sanda domin yi mata tambayoyi.”

Darakten ya sanar da cewa bayan an kai al’amarin ofishin yan sanda, an umurci mahaifin yaron daya kawo yaron yayinda mahaifiyar ke garkame a ofishin yan sandan.

Oseni tace za’a gurfanar da matar a kotu ranar Talata, 3 ga watan Maris.

A yanzu an kai yaron ma’aikatar cigaban matasa da wayar da kan al’umma domin kaishi asibiti .

Za’a hukunta mahaifiyar da ta yiwa danta jina-jina a Legas
Za’a hukunta mahaifiyar da ta yiwa danta jina-jina a Legas
Asali: Depositphotos

A wani labari mai kama da haka, Kelvin Ogheneogaga, dalibin wata makarantar sakandire, Ekiugbo Grammar School, da ke karamar hukumar Ughelli ta arewa a jihar Delta, ya rasa ransa sakamakon dukan da ake zargin malaminsa ya yi masa.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa daliban makarantar sun barke da zanga-zanga a ranar 26 ga watan Fabrairu sakamakon mutuwar dalibin.

Fusatattun daliban sun far wa malamin da ya bugi marigayin, sun lalata ofishin shugaban makarantar tare da jifan motar 'yan sanda.

Wata majiya da ta nemi a boye sunanta ta bayyana cewa sai da daliban suka sanar da malamin cewa Kelvin bashi da koshin lafiya, sakamakon wani rauni da ya samu a kafarsa, amma duk da haka malamin ya cigaba da bugunsa kamar Allah ya aiko shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel