Yanzu-yanzu: Coronavirus ta bulla a kasar Tunisiya da Senegal

Yanzu-yanzu: Coronavirus ta bulla a kasar Tunisiya da Senegal

Kasar Tunisiya da da kasar Senegal sun tabbatar da bullar cutar Coronavirus na farko, hakan ya ya kai adadin kasashen da ta bulla a nahiyar Afrika biyar.

Gabanin shigarta kasashen nan biyu a yau Litinin, kasashen Misra, Algeria, da Najeriya sun tabbatar da bullar cutar da ta hallaka akalla mutane 3000 a fadin duniya.

A wani hira da manema labarai da ministan kiwon lafiyan kasar Senegal, ya shirya a birnin Dakar ranar Litinin, ya bayyana cewa wani dan kasan Faransa ya shigo da cutar kasar.

A kasar Tunisiya kuwa, wani dan kasar Italiya ne ya jajubo musu cutar.

Yanzu-yanzu: Coronavirus ta bulla a kasar Tunisiya da Senegal
Yanzu-yanzu: Coronavirus ta bulla a kasar Tunisiya da Senegal
Asali: Twitter

A gida Najeriya kuwa, Adadin wadanda aka gano kuma aka killace da ake zargin sun gana da dan kasar Italiyan da ya kawo cutar coronavirus Najeriya a kamfanin siminti dake Ewekoro, jihar Ogun sun tashi daga 28 zuwa 39.

Shugaban masana'antar, Segun Soyoye, ya bayyana hakan ranar Asabar.

Soyoye ya kara da cewa ba'akulle kamfanin ba sabanin abinda ake yadawa a kafafen yada labarai.

Segun Soyoye ya laburta hakan ne yayinda jami'an cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC da kungiyar kiwon lafiyar duniya WHO suka kai ziyara kamfanin ranar Asabar, 29 ga Febrairu, 2020.

Ya kara da cewa an kawo dan kasar Italiyan kamfanin ne dake Ewekoro domin duba wasu na'urori da aka sayo daga kasar Sweden.

Ya ce an killace dukkan mutanen 39 a cikin kamfanin kuma zasu kwashe kwanaki 14 a ciki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel