Yadda tsofin gwamnonin jihohin arewa uku suka kirkiri Boko Haram - Musa Dikwa

Yadda tsofin gwamnonin jihohin arewa uku suka kirkiri Boko Haram - Musa Dikwa

Wani babban malamin addinin Kirista dan asalin jihar Borno, Rabaran Kallamu Musa Dikwa, ya ce wasu tsofin gwamnonin jihohin arewa guda uku ne suka kirkiro kungiyar Boko Haram jim kadan bayan dawowar mulkin dimokradiyya a shekarar 1999.

Malamin, babban darekta a cibiyar tabbatar da adalci a tsakanin addinai da kabilun Najeriya, ya yi ikirarin cewa ya aika sakonni ga daidaikun mutane da kuma kafafen yada labarai da ke cikin Njeriya a kan yunkurin kafa kungiyar ta'addancin tun a wancan lokacin.

"An fara kirkirar kungiyar Boko Haram ne a shekarar 2000. Na aika sakonni ga wasu mutane da kuma kafafen yada labarai a wancan lokacin don ankarar da su abinda ke faru wa. Bayan Obasanjo ya hau mulki a shekarar 1999, ya nada shugabannin rundunonin tsaro na kasa, kuma dukkansu sun fito ne daga yankin arewa ta tsakiya - Benuwe, Filato, Kogi da Kwara. Saboda kasancewar dukkansu mabiya addinin Kirista ne, sai gwamnonin arewa guda uku suka hada kai domin kirkirar wasu tsageru da zasu yi wa addinin Musulunci aiki, saboda sun ji haushin rashin dan kabilar Hausa ko Fulani Musulmi daga cikin shugabannin tsaro da Obasanjo ya nada. Wadannan gwamnoni sun yi karo-karo na miliyan N100 kowannensu domin saya wa tsagerun kayan aiki, daga nan ne kuma aka fara samun rigingimun addini a arewa.

"Bayan sun hada wa tsagerun matasan Islama kudin ne aka fara samun rikicin addini a Kaduna, Kano, Jigawa da Zamfara da sunan bukatar kafa shari'ar Musulunci. Niyyarsu ita ce kawai su firgita mabiya addinin Kirista, su kuma danne su a yankin arewa. Sun fara kai hare-hare a Coci tare da kashe mana mutane. Duk lokacin da aka gudanar da zabe basu samu yadda suke so ba, sai su fara kone Coci da kashe Kirsitoci. Basa kone ofishin jam'iyyu ko na hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).

Yadda tsofin gwamnonin jihohin arewa uku suka kirkiri Boko Haram - Musa Dikwa
Rabaran Kallamu Musa Dikwa
Asali: Twitter

"Wadannan tsagerun matasa sun fito a shekarar 2006 sun ce shari'ar Musulunci suke so a kaddamar a Maiduguri bayan gwamnan jihar Borno a lokacin ya ki basu hadin kai. A shekarar ne kuma aka yi wani hoton batanci ga addinin Musulunci a kasar Denmark, amma wadannan matasa sai da suka kone Coci 66 a Borno tare da kashe Kiristoci masu dumbin yawa kafin daga bisani su koma bi gida - gida, Coci zuwa Coci, amma babu wanda ya yi magana - mu ne kadai muke magana tare da yin korafi a kan abinda yake faruwa," kamar yadda jaridar Punch ta rawaito cewa Musa Dikwa ya fada.

Sannan ya kara da cewa, matasan sun kone Coci 27 a watan Yuli n shekarar 2009 tare da kashe mabiya addinin Kirsita masu yawa, amma basu taba wani Musulmi ko wata Musulma ba sai dai idan jami'an tsaro ne.

DUBA WANNAN: A karon farko: Shugaba Buhari ya yi magana a kan bullar 'Coronavirus' a Najeriya

"Tun daga shekarar 2009 har 2014 sun cigaba da kai hare-hare a Coci tare da bi gida - gida suna yanka Kiristoci. A cikin shekarar 2014 ne suka fara kai hari a kan Musulmai saboda shugabanni sun ki basu hadin kai wajen yakar wadanda ba Musulmai ba da ke arewa. Sun yanka manyan malamanmu masu mukamin 'rabaran' guda hudu a shekarar 2009," a cewarsa.

Da aka tambaye shi ko yana da wata hujja da zai iya kare kansa da ita a kan abubuwan da ya fada, sai Musa Dikwa ya ce, "mu na da faifan VCD fiye da 20 na Malaman Islama da ke ikirarin cewa zasu yaki Kiristoci idan Musulmi dan arewa bai samu mulki ba. Wani fitaccen malamin addini ya taba ingiza matasan Musulmai cewa kar su mutunta duk wani shugaban kasa idan ba Musulmi ba ne. Mu na da faifan bidioyonsa a cikin harshen Hausa. Ya yi ikirarin cewa duk tsofin shugabannin kasa da suka mutu, a ciki har da Umaru Yar'adua, arna ne suka kashe su, a saboda haka ba za su bar duk wanda ba Musulmi ba ya sake mulkin Najeriya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel