Kisan kiyashi a Kaduna: El-Rufai ya lashi takobin share yan bindiga daga doron kasa

Kisan kiyashi a Kaduna: El-Rufai ya lashi takobin share yan bindiga daga doron kasa

Gwamnan jahar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai ya yi alkawarin share duk wasu yan bindiga dake jahar Kaduna daga doron kasa biyo bayan wani mummunan hari da suka kai a ranar Lahadi inda suka kashe mutane 51.

Miyagun yan bindiga sun kai mummunar hari a ranar Lahadi, 1 ga watan Maris inda suka kashe mutane da dama a kananan hukumomin Igabi da Giwa, sa’annan suka kona gidaje da motoci da dama, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

KU KARANTA: An sake kwatawa: Yan bindigan daji sun hallaka dakacin kauye a Zamfara

Kisan kiyashi a Kaduna: El-Rufai ya lashi takobin share yan bindiga daga doron kasa
El-Rufa yayin ziyarar kauyukan
Asali: Facebook

Majiyoyi sun bayyana cewa harin ya yi kama da harin ramuwar gayya sakamakon yan bindigan suna zargin al’ummomin yankunan da suka kai ma hari da baiwa jami’an tsaro bayanan sirri game da ayyukansu.

Sai dai gwamnan jahar Kaduna El-Rufai ya dauki alkawarin kawo karshen hare haren yan bindiga a jahar, El-Rufai ya bayyana haka ne yayin wata ziyara da ya kai zuwa yankunan da hare haren ya shafa, inda ya dage a kan lallai ba zai taba yi ma yan bindiga afuwa ba.

Gwamnan ya baiwa mazauna kauyukan tabbacin cewa za’a jibge Sojoji a kauyukan domin su basu tsaro, amma al’ummar kauyen sun shaida ma gwamnan cewa yan bindigan sun shigo ne daga jahar Katsina.

Kisan kiyashi a Kaduna: El-Rufai ya lashi takobin share yan bindiga daga doron kasa
El-Rufa yayin ziyarar kauyukan
Asali: Facebook

A wani labari kuma, gungun miyagu yan bindiga sun kaddamar da mummunar hari a cikin karamar hukumar Dansadau na jahar Zamfara, inda suka kashe wani sarakunan gargajiya biyu muhimmanci kamar yadda rundunar Yansandan jahar ta tabbatar.

Mai magana da yawun rundunar, SP Mohammed Shehu ne ya bayyana haka a ranar Litinin, 2 ga watan Feburairu inda yace yan bindigan sun kashe Alhaji Gambo Kujemi, dakacin kauyen Kujemi.

Haka zalika, SP Mohammed Shehu ya kara da cewa baya ga kisan dakacin, yan bindigan sun kashe wani mutum daya a yayin da suka kai farmaki a kauyen Karauchi, a karamar hukumar Dansadau, inda a can ne harin ya rutsa da Gambo Kujemi, dakacin Kujemi.

A cewar Shehu yan bindigan sun kai farmakin na da yawansu a kan babura da misalin karfe 8:40 na daren Lahadi, inda suka yi ta harbe harben mai kan uwa da wabi, inda suka kashe har dakacin Karauchi, Mustapha Halilu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel