Yanzu-yanzu: Kuma dai, an dage zaman sake duba shari'ar gwamnan Imo a kotun koli

Yanzu-yanzu: Kuma dai, an dage zaman sake duba shari'ar gwamnan Imo a kotun koli

Kotun koli, a ranar Litinin, ta sake dage zaman sauraron bukatar jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, da dan takararta Emeka Ihedioha na sake duba shari'ar zaben gwamnan jihar Imo.

Kotun ta ce a dawo gobe (Talata) domin cigaban da zaman.

Kwamitin Alkalan kotun bakwai dake sauraron karar karkahsin shugaban Alkalan Najeriya, Tanko Muhammad, ta dage karar ne bayan lauyan Emeke Ihedioha, Cif Kanu Agabi SAN, ya bukaci karin lokaci domin duba takardun da gwamnan Imo, Hope Uzodinma da jam'iyyar All Progressive Congress, APC, suk bashi a cikin kotu.

Yace: "Ya masu girma masu shari'a, an dage karar nan a baya amma kuma yanzu nan aka bamu wasu takardu daga gwamna Imo da Jam'iyyar APC)

"Idan babu takura gareku masu shari'a, a bamu daman dawowa gobe (Talata) saboda mu samu duba takardun"

A bangaren lauyan Uzodinma da APC, Damian Dodo SAN, ya ce sun shirya tsaf a cigaba da zaman shari'a. Hakazalika lauyan INEC, Tanimu Inuwa SAN, ya ce sun shirya.

Amma shugaban Alkalan Najeriya, ya dage zaman zuwa ranar Talata.

Yanzu-yanzu: Kuma dai, an dage zaman sake duba shari'ar gwamnan Imo a kotun koli
kotun koli
Asali: UGC

A bangare guda, Kotun koli, a ranar Litinin, ta sake dage zaman sauraron bukatar jam'iyyar All Progressives Congress APC inda ta bukaci kotun koli ta sake duba shari'ar da ta yanke ranar 24 ga Mayun, 2019 inda ta kwace dukkan kujerun da yan takaran suka lashe a jihar Zamfara.

Kotun ta ce a dawo ranar 17 ga Maris domin cigaban da zaman.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel