Wani mutum ya kashe makwabcinsa dattijo a kan batan wayar hannu

Wani mutum ya kashe makwabcinsa dattijo a kan batan wayar hannu

Wani matashi mai shekaru 27 a jihar Ogun ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar. Ejike Okata ya yi sanadiyyar mutuwar makwabcinsa mai suna Obalende ne da ke Ijebu-Ode a jihar.

A wata takardar da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ya fitar, ya ce wanda ake zargin ya halaka makwabcinsa mai shekaru 50.

Kamar yadda Oyeyemi ya sanar, "ya sassara makwabcinsa da adda a kan karamar hayaniya kuma wanda ake zargin ya tsere tun bayan aukuwar lamarin."

Ya yi bayanin cewa, an kama Okata ne bayan rahoton da wani kaninsa ya kai wa 'yan sandan Obalende a ranar 28 ga watan Fabrairun 2020.

"Bayan samun rahoton, DPO din Obalende, SP Omoniji Sunday ya tura jami'ai inda abun ya faru kuma an mika gawar zuwa ma'adanar gawawwakin babban asibitin Ijebu Ode. An kuma baza jami'an don damko wanda ake zargin sakamakon guduwar da yayi." ya ce.

Wani mutum ya kashe makwabcinsa dattijo a kan batan wayar hannu
Wani mutum ya kashe makwabcinsa dattijo a kan batan wayar hannu
Asali: Depositphotos

DUBA WANNAN: Fitattun 'yan siyasa 12 da suka mutu sakamakon hatsarin mota

"Kokarin jami'an ya yi amfani a ranar 1 ga watan Maris na 2020 yayin da wanda ake zargin ke kokarin hawa mota don barin garin." Ya ce.

Bayan damke shi, wanda ake zargin ya amsa laifinsa na halaka dattijon ne bayan ya zargesa da satar masa waya.

A yanzu dai, Kwamishinan 'yan sandan jihar, Kenneth Ebrimson, ya bada umarnin mika lamarin ga sashi na musamman na binciken laifukan kisan kai, don bincike don gurfanarwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel