A karon farko: Shugaba Buhari ya yi magana a kan bullar 'Coronavirus' a Najeriya

A karon farko: Shugaba Buhari ya yi magana a kan bullar 'Coronavirus' a Najeriya

Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi kira ga 'yan Najeriya a kan kada su tsorata kan barkewar cutar Coronavirus.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Najeriya ta bayyana samun mai cutar a makon da ya gabata. Wani dan kasar Italiya ne ya iso Najeriya da cutar kuma aka killace shi.

Cutar ta jawo halakar kusan mutane 3,000 a duniya, inda mafi yawa an mutu ne a kasar China inda cutar ta fara.

A wata takardar da mai magana da yawun fadar shugaban kasar, Garba Shehu ya fitar, ya ce Buhari yayi kira ga 'yan Najeriya "a kan kada su tsorata da sabuwar cutar Covid-19 din da ta shigo kasar nan."

Ga cikakkiyar takardar:

Da tsananin alhini Shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jajanta shigowar cutar Covid-19 a jihar Legas da ke Najeriya.

Akwai kokari da jajircewar gwamnatocin jihohi wajen kafa cibiyoyin gaggawa da kuma hanyoyin kare yaduwar cutar.

A karon farko: Shugaba Buhari ya yi magana a kan bullar 'Coronavirus' a Najeriya
A karon farko: Shugaba Buhari ya yi magana a kan bullar 'Coronavirus' a Najeriya
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Fitattun 'yan siyasa 12 da suka mutu sakamakon hatsarin mota

A don haka shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjinawa kokarin ma'aikatar lafiya ta tarayya da sauran cibiyoyi a kan jajircewarsu da kwarewarsu wajen bankado cutar. Sun dau matakin gaggaawa wajen gano wadanda mai cutar yayi mu'amala da su.

Shugaban kasar ya jinjinawa ma'aikatar lafiya ta tarayya da kuma gwamnatin jihohin Legas da Ogun da suka kai rahoton lamarin kuma suka jawo hankulan jama'a tare da wayar musu da kai.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga 'yan Najeriya da su saurari shawarwarin ma'aikatar lafiya da cibiyar kiwon lafiya ta duniya.

An watsa wannan ne a duk kafafen yada labarai daga ma'aikatar yada labaran Najeriya.

Garba Shehu

Babban mai bada shawara ga shugaban kasa a kan yada labarai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel