NNPC ta fara sarrafa bakin mai na Najeriya da kanta, ya shiga kasuwa

NNPC ta fara sarrafa bakin mai na Najeriya da kanta, ya shiga kasuwa

Kamfanin man fetir ta Najeriya, NNPC ta kaddamar da sabon bakin mai dan Najeriya wandata sarrafa shi da kanta domin amfanin yan Najeriya masu amfani da motoci wajen zirga zirgarsu, ini rahoton kamfanin dillancin labarun Najeriya.

Shugaban kamfanin NNPC Retail Ltd, Billy Okoye ne ya bayyana haka a babban birnin tarayya Abuja yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Lahadi, inda yace a Najeriya aka hada man kuma don amfanin yan Najeriya.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Dan kwallon Najeriya ya kamu da cutar Coronavirus

NNPC ta fara sarrafa bakin mai na Najeriya da kanta, ya shiga kasuwa
NNPC ta fara sarrafa bakin mai na Najeriya da kanta, ya shiga kasuwa
Asali: Facebook

Ya bayyana sunayen samfurin bakin man guda shida kamar haka; Nitro Diamond, Nitro Gold, Nitro Super 40, Nitro 2, Rhino X da Rhindo HD, ya kara da cewa kamfanin NNPC ya samu kayan hade haden bakin man daga manyan kamfanonin sinadari na duniya.

“An hada man NNPC ne ta hanyar amfani da kayan hadi wanda duniya ta aminta da su domin ya inganta aikin injinan ababen hawa yadda ya kamata. Bincikenmu ya nuna yan Najeriya na son amfani da man su, sa’annan yawancin matsalar da ababen hawa suke fama dasu a Najeriya a sanadiyyar rashin ingantaccen bakin mai a injinansu ne, shi yasa muka sarrafa wannan.” Inji shi.

Okoye ya kara da cewa tun a ranar 28 ga watan Nuwambar 2019 suka kaddamar da man, amma basu fitar da shi kasuwa ba sai da suka gudanar da gwaje gwaje a ababen hawa domin tabbatar da ingancinsa da kuma karbuwarsa.

A wani labarin kuma, wata mata dattijuwa mai shekaru 70 a duniya, wanda aka sakaya sunanta, ta jagoranci matasa mafarauta zuwa cikin dazuka inda suka kashe yan bindiga 40 a jahar Neja.

Guda daga cikin mafarautan dake cikin tawagar wannan jaruma, Mallam Alhassan ya bayyana cewa ta jagorance su zuwa cikin dajin Zuguruma a karamar hukumar Mashegu na jahar, inda a can suka yi artabu da yan bindiga.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel