Mace mai kamar Maza: Tsohuwa yar shekara 70 ta yi sanadiyyar mutuwar yan bindiga 40

Mace mai kamar Maza: Tsohuwa yar shekara 70 ta yi sanadiyyar mutuwar yan bindiga 40

Masu iya magana kan ce “Mace mai kamar maza kwari ne babu” wannan magana na masu hikima ya tabbata a kan wata mata dattijuwa mai shekaru 70 a duniya, wanda aka sakaya sunanta, da ta jagoranci matasa mafarauta zuwa cikin dazuka inda suka kashe yan bindiga 40 a jahar Neja.

Jaridar Blueprint ta ruwaito guda daga cikin mafarautan dake cikin tawagar wannan jaruma, Mallam Alhassan ya bayyana cewa ta jagorance su zuwa cikin dajin Zuguruma a karamar hukumar Mashegu na jahar, inda a can suka yi artabu da yan bindiga.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Dan kwallon Najeriya ya kamu da cutar Coronavirus

A cewar Alhassan, shigarsu dajin ke da wuya sai suka fara harbe harbe a sama da nufin janyo yan bindigan daga mabuyarsu a wani sabon salon dabarar yaki. “Suna fitowa sai suka dinga harbin mai kan uwa da wabi ba tare da wani takamaimen inda suke harbi ba.

“A haka har harsashinsu ya kare, daga nan muka dira a kansu har sai da muka kashe guda 40, mun kwato bindigu samfuri daban daban da sauran makamai wanda muka mika hukumar Yansanda.” Inji shi.

Sai dai da majiyar Legit.ng ta tuntubi hukumar Yansandan jahar domin tabbatar da labarin, sai ta ce ba zata ce komai ba a yanzu sakamakon har yanzu ana cigaba da kaddamar da hare haren.

A nata bangaren, gwamnatin jahar Neja ta jinjina ma namijin kokarin da mafarautan suke yi tun bayan da gwamnan jahar, Abubakar Sani Bello ya amince da sanyasu cikin harkar tabbatar da tsaro tare da yaki da yan bindiga.

Mai magana da yawun gwamnan, Mary Noel Barje ce ta tabbatar da haka inda ta ce gwamnan ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a taron al’ummar Zuru, inda ya jinjina ma kokarin mafarautan, ya ce hakan ya zama wajibi duba da rikicin da yan bindiga suke haifarwa a jahar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel