Mutane 8 da Buhari ya sallama daga gwamnatinsa a zango na biyu
Gwamantin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fuskanci sallamar tare da cire ma’aikata. A yayin da wasu aka salllamesu saboda almundahana wacce ta hada da rashawa, wasu an sallamesu ne saboda wa’adin mulkinsu ya cika kuma basu nemi damar ci gaba ba. Ga wasu daga cikin wadanda aka sallama a zangon mulkin Buhari na biyu.
1. Farfesa Charles Dokubo: Shi ne tsohon shugaban shirin rangwame na yankin Niger Delta.

Asali: Facebook
2. Barista Bisi Adegbuyi: Shi ne shugaban hukumar NIPOST ta Najeriya.

Asali: Twitter
3. Dr. Pius Odubu: Shi ne shugaban hukumar NDDC kuma dan asalin jihar Edo ne. Shugaban hukumar na rikon kwarya, Joy Nunieh shi ma an sallamesa kuma an maye gurbinsa da Farfesa Kemebradikumo Daniel Pondei.
4. Dr. Muiz Banire: Shi ne shugaban hukumar kula da kadarorin kasar nan (AMCON).

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Zargin zagin gwamnan APC: An tsare Atiku Boza na PDP a kurkuku, an garkame wanda ya je belinsa
5. Babatunde Fowler: Shi ne shugaban hukumar kudin shiga ta tarayya (FIRS).

Asali: UGC
6. Mrs Winifred Oyo-Ita: Ita ce tsohuwar shugaban aiyukan gwamnati na tarayya.

Asali: UGC
8. Rev. For Ujah: Shi ne sakataren hukumar hajjin Kirstoci (NCPC).
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng