Fitattun 'yan siyasa 12 da suka mutu sakamakon hatsarin mota

Fitattun 'yan siyasa 12 da suka mutu sakamakon hatsarin mota

A Najeriya dai mutane da dama na rasa rayukansu sakamakon hadurra a kan titunan kasar. Hadurra kuwa na faruwa ne saboda rashin kyan tituna da lalacewarsu. Sau da yawa dai jama'a na kokawa da yadda wasu titunan kasar nan suka lalace. Ga wasu sanannun 'yan siyasa da suka rasa rayukansu sakamakon hadurra a kan titunan Najeriya.

1. Adegoke Adelabu

Yana daya daga cikin ‘yan siyasar farko na Najeriya da ya rasu sakamakon hatsarin mota. Shine shugaban NCNC kuma tsohon dan siyasa a yankin yammacin kasar nan. Abokin adawar Chief Obafemi Awowolo ne wanda ya kirkiro Action Group.

2. Dr. Joe Ukpo

Dan kasa ne nagari kuma ma’aikacin gwamnati. Ya rasu ne sakamakon mummunan hatsarin motar da ya faru a ranar 15 ga watan Afirilun 2018. An gano cewa yana kan hanyarsa ta zuwa Okpoma/Okuku a jihar Cross River daga Abuja. Ya mutu bayan sa’o’i kadan da aukuwar hatsarin.

3. Dr. Matthew Achigbe

Shine shugaban jam’iyyar APC na jihar Cross River. Ya rasa ransa ne sakamakon hatsarin motar da ya faru a ranar 16 ga watan Nuwamban 2018 a kan titin Afikpo da ke jihar Ebonyi. Yana kan hanyar zuwa coci ne da ke jihar Enugu.

4. Chief James Ocholi (SAN)

Ya yi karamin ministan kwadago. Ya rasu ne tare da matarsa da kuna dansa a mummunan hatsarin da ya faru a ranar 16 ga watan Maris 2016. Hatsarin ya auku ne a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

5. Sakiru Alabi Balogun

Sakiru dan takarar shugabancin karamar hukumar Ikotun/Igando ne a karkashin jam’iyyar APC. Ya rasu ne a hatsarin ranar 21 ga watan Yulin 2017 a kan titin LASU/Isheri da ke yankin Igando. An gano cewa komai na kamfen dinsa na tafiya dai-dai a lokacin da ya rasa rayuwarsa.

6. Genera John Shagaya

Shi ne tsohon ministan al’amuran cikin gida. Ya rasu ne a hatsarin motar da ya faru na ranar 11 ga watan Fabrairun 2018. Ya rasu yana da shekaru 75 a duniya.

Fitattun 'yan siyasa 12 da suka mutu sakamakon hatarin mota
Fitattun 'yan siyasa 12 da suka mutu sakamakon hatarin mota
Asali: UGC

7. Alhaji Auwal Jallah

Alhaji Auwal Jallah ne mai magana da yawun jam’iyyar APC ta jihar Bauchi. Ya rasu ne a hatsarin da ya auku na ranar 4 ga watan Disamban 2017. Lamarin ya auku ne a kan babban titin Azare zuwa Gamawa na jihar Kano.

8. Sanata Usman Bashir

Tsohon dan majalisar dattijan ne daga jihar Yobe. Ya rasu ne a hatsarin da aka tafka na ranar 2 ga watan Yulin 2012 a kan titin kano zuwa Zaria.

9. Olufunsho Martins (AVM)

Ya rasu ne a ranar 28 ga watan Oktoban 2017. Ya yi hatsarin ne a kusa da jami’ar jihar Legas. Hatsarin ya kai ga har motarsa ta fada cikin ruwan kogin Legas amma daga baya an samo gawarsa a ciki.

10. Hajiya Aisha Tahir

Ita ce shugaban mata ta jam’iyyar APC a karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa. Ta rasu ne tare da wasu mutane shida na jam’iyyar a ranar 23 ga watan Janairun 2019. Sun dawo daga gangamin kamfen ne a jihar.

11. Sanata Mukhtar Abdulkarim

Dan asalin jihar Zamfara ne daga karamar hukumar Talatan Mafara amma an haifesa a garin Zurmi ne. Ma’aikacin gwamnati ne, dan siyasa, malami kuma mai habaka al’adu. Ya rasu ne tare da dan uwansa da kuma direbansa a hatsarin ranar 23 ga watan Disamba. Babbar mota ce ta nikesu a kan titi.

12. Abdulkareem Adisa

Shine tsohon gwamnan jihar Oyo a zamanin mulkin soja. Ya rasu ne a wani asibitin da ke London sakamakon hatsarin mota da yayi. Dan asalin jihar Kwara ne kuma yana cikin wadanda ake zargi da sa hannu a mutuwar marigayi Sani Abacha.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel