Coronavirus: Adadin wadanda aka killace a Ogun ya kai 39

Coronavirus: Adadin wadanda aka killace a Ogun ya kai 39

Adadin wadanda aka gano kuma aka killace da ake zargin sun gana da dan kasar Italiyan da ya kawo cutar coronavirus Najeriya a kamfanin siminti dake Ewekoro, jihar Ogun sun tashi daga 28 zuwa 39.

Shugaban masana'antar, Segun Soyoye, ya bayyana hakan ranar Asabar.

Soyoye ya kara da cewa ba'akulle kamfanin ba sabanin abinda ake yadawa a kafafen yada labarai.

Segun Soyoye ya laburta hakan ne yayinda jami'an cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC da kungiyar kiwon lafiyar duniya WHO suka kai ziyara kamfanin ranar Asabar, 29 ga Febrairu, 2020.

Ya kara da cewa an kawo dan kasar Italiyan kamfanin ne dake Ewekoro domin duba wasu na'urori da aka sayo daga kasar Sweden.

Ya ce an killace dukkan mutanen 39 a cikin kamfanin kuma zasu kwashe kwanaki 14 a ciki.

A cewarsa: "Adadin wadanda suka hadu da shi sun kai 39 kuma mun killacesu. mun garkame gida, asibiti da motocin."

"Bamu son yi wani ganganci shi yasa mukayi haka. Yau kwana na uku kenan, zasu yi kwanaki 14, kuma zamu rika lura da su."

"Akwai likita a nan kuma aikinsa shien dubasu a koda yaushe, a yanzu dai kowa na cikin koshin lafiya, babu alamu tattare da su, muna basu dukkan abinda suke bukata."

Coronavirus: Adadin wadanda aka killace a Ogun ya kai 39
Coronavirus: Adadin wadanda aka killace a Ogun ya kai 39
Asali: UGC

A bangare guda, An killace yan kasar Sin uku da ake zargin suna dauke da cutar coronavirus a karamar hukumar wase dake jihar Plateau, tsakiyar Najeriya.

Kwmaishanan kiwon lafiyar jihar, Nimkong Ndam, wanda tabbatar da hakan ya ce yan kasar Sin sin sun shiga jihar ne ranar Jumaa daga kasar Habasha. Sun zo jihar aikin hkar maadinai.

Ya ce tuni an killaceus a wata cibiya domin likitoci da masan kiwon lafiya su gudanar da bincike kansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel