Tsoho mai shekaru fiye da 100 ya auri budurwa 'yar 20 (Hotuna)

Tsoho mai shekaru fiye da 100 ya auri budurwa 'yar 20 (Hotuna)

Wani mutum wanda aka gano yana da shekaru 100 a duniya ya auri wata karamar yarinya wacce take cikin shekarunta na 20.

Masoyan sun yi auren ne a kasar Indonesia da ango mai suna Katte wanda yayi jika da amaryar. nagon ya kasance wanda ya halarci yaki a lokacin mulkun mallakar Dutch a karnin da ya gabata.

An yi bikin ne a gidan amarya mau suna Indo Alang da ke Wajo a tsakiyar kasar Indonesia a yankin Kudancin Sulawesi.

A yayin zantawa da wata jaridar kasar mai suna mgidan dia, Ayu Anggreni Muchtar, wani dan uwan dattijon angon, ya ce duk da ba a san takamaiman shekarun angon ba, akwai tabbacin cewa ya zarta shekaru 100.

Tsoho mai shekaru fiye da 100 ya auri budurwa 'yar 20 (Hotuna)
Tsoho mai shekaru fiye da 100 ya auri budurwa 'yar 20 (Hotuna)
Asali: Twitter

"Ba ni da tabbacin shekarunsu amma Katte gaskiya ya wuce shekaru 100 a duniya. Ya yi yaki a llokacin mulkin malllakar Dutch. Matarsa kuwa tana cikin shekarunta na 20."

Tsoho mai shekaru fiye da 100 ya auri budurwa 'yar 20 (Hotuna)
Tsoho mai shekaru fiye da 100 ya auri budurwa 'yar 20 (Hotuna)
Asali: Twitter

An gano cewa Katte ya kashe fam 276 wanda yayi dai-dai da IDR miliyan 5 don auren matar shi din. Kudin ana biyansu ne daga ango zuwa amaryarsa da kuma danginta don yin auren a Musulunce.

Tsoho mai shekaru fiye da 100 ya auri budurwa 'yar 20 (Hotuna)
Tsoho mai shekaru fiye da 100 ya auri budurwa 'yar 20 (Hotuna)
Asali: Twitter

Irin wannan auren mai tsananin tazarar ba kasafai ake yin sa a kasar Indonesia amma kuma idan aka yi, ana samun babbar tazara tsakanin angon da amaryar.

Tsoho mai shekaru fiye da 100 ya auri budurwa 'yar 20 (Hotuna)
Tsoho mai shekaru fiye da 100 ya auri budurwa 'yar 20 (Hotuna)
Asali: Twitter

Cikin kwanakin nan ne jaridun kasar suka ruwaito yadda aka yi wani bikin aure tsakanin wata mata mai shekaru 71 da kuma yaro mai shekaru 16.

A dokar kasar dai, karancin shekarun aure shine 16.

Amma kuma wata dokar da ta bar baraka a kasar ita ce yadda aka amincewa komai tsufan namiji ya auri yarinya duk kankantarta.

Da sama da auren yara da ake yi kanana suka kai miliyan 1.5, UNICEF ta bayyana cewa kasar ce kasa ta takwas a duniya wacce ke da kashi 14 na auren yara kasa da shekaru 18 a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel