An mayar da dan Italiyan da kawo Coronavirus Najeriya sabuwar asibiti bayan kokarin arcewa da yayi
A ranar Asabar, gwamnatin jihar Legas ta mayar da dan kasar Italiyan da ya kawo cutar Coronavirus Najeriya sabuwar asibiti domin cigaba da kula da shi.
Haka ya biyo bayan kukan da baturen yayi kan rashin kyawun asibitin da aka ajiyeshi inda yayi yunkurin arcewa.
A cewar kwamishanan kiwon lafiyar jihar, Farfesa Akin abayomi, an mayar da dan Italiyan cibiyar kula da cututtuka a asibiti Yaba.
Yace, “Muna gyaran wani sashen asibiti, shi yasa muka ajiyeshi a wani daki daya, amma mun daukeshi daga wajen zuwa daya daga cikin wuraren da muka kammala gyarawa da cikakken kayayyakin aiki. “
“Yana can yanzu kuma ya gamsu.“
“Zuwa safiyar yau (Asabar), ya fara samun saiki, babu wasu sabbin alamomin rashin lafiya tattare da shi amma har yanzu akwai sauran zazzabi, zamu sake gwadashi domin sanin yadda cutar ke jikinshi.“

Asali: Twitter

Asali: Twitter
KU KARANTA Coronavirus: An killace yan kasar Sin 3 a jihar Plateau
Mun kawo muku rahoton cewa biyo bayan gano mai dauke da muguwar cuta ta Coronavirus a Najeriya tare da kebance mai cutar a asibitin Yaba da ke Legas, wani ma'aikacin Lafiya a ranar Juma'a ya ce mara lafiyan ya fusata kuma ya yi yunkurin guduwa.
Mara lafiyan ya nuna damuwar shi a kan yadda wajen da aka kebance shi yake, wata majiya ta ce.
Wani babban ma'aikacin lafiya da ya yi magana da wakilin jaridar The Punch a ranar Juma'a, ya jajanta yadda wajen yake. Ya ce "hukumomi ba su cika alkawarin da suka dauka ba."
Majiyar ta ce babu wani shiri da jihar Legas din tayi a kan wannan cutar.
Kamar yadda wata majiya ta tabbatar, gwamnatin jihar Legas din ba ta da wajen adana wadanda suka yi mu'amala da mutumin da ke dauke da cutar.
Kamar yadda majiyar ta sanar, waje daya ne aka tanadar don adana wadanda ake zargi suna dauke da cutar da kuma wadanda aka tabbatar da cewa suna dauke da ita. A hakan kuwa gyaran wajen ake yi don bai kammala ba.
Majiyar ta zargi cewa, dakin an kwashe marasa lafiya daga ciki ne kuma an kange dakin ne da jan kyalle.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng