Hana bara a Kano: Sheikh Isa Pantami ya bayyana matsayinsa
- Ministan harkokin sadarwa, Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana rashin amincewarsa da malaman addinin Islama da ke sukar dokar hana bara a jihar Kano
- Pantami, shehin malamin addinin Islma kafin a bashi minista, ya yi kira ga malaman addinin a kan su rungumi tsarin tattauna wa domin warware kowacce matsala
- Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai a wurin wani taron shirin yaye dalibai da kwalejin kimiyya ta Kano ta shirya
A ranar Juma'a ne ministan harkokin sadarwa, Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana rashin amincewarsa da malaman addinin Islama da ke sukar dokar hana bara a jihar Kano da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kaddamar.
Ministan ya bayyana matsayarsa ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kadan bayan ya kammala gabatar da takarda a wurin wani taron shirin yaye dalibai da kwalejin kimiyya ta Kano (Kano State Polytechnic) ta shirya ranar Juma'a.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Abba Anwar, sakataren yada labaran gwamnan jihar Kano, ya fitar.

Asali: UGC
"A fahimtar da nake da ita a kan wannan batu, ba daidai bane a wurin malaman addini su fito suna kalubalantar gwamna haka kawai. Kamata ya yi su zo a zauna tare da su domin nemo mafita a kan lamarin.
DUBA WANNAN: Hukuncin kotu: An kashe mayakan kungiyar Boko Haram 10 ta hanyar bude musu wuta
"Saboda babu shakka mayar da yaran da ke bara makaranta shine mafi alheri a garesu, ga iyayensu da ma al'umma baki daya. A bangaren gwamnati, alhakin shugaba ne ya tabbatar da cewa jama'arsa sun samu rayuwa mai nagarta," a cewar Pantami, kamar yadda ya ke a cikin sanarwar da Anwar ya fitar.
Pantami, fitaccen malamin addinin Islma kafin ya zama minista, ya yi kira ga malaman addinin a kan su rungumi tsarin tattauna wa domin warware kowacce matsala. "Amma fa shawara ce kawai," in ji Pantami.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng