Coronavirus: Gwamnatin jihar Zamfara ta fasa kai dalibai 20 karatu a China

Coronavirus: Gwamnatin jihar Zamfara ta fasa kai dalibai 20 karatu a China

Gwamnatin jihar Zamfara ta soke tafiyar dalibai 20 da ta dauka nauyin karatunsu zuwa kasar China a karkashin tallafin gwamnatin jihar. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa Gwamna Belllo Matawalle ya sama wa dalibai 200 na jihar gurbin karatu a makarantu daban-daban na fannin kimiyya da fasaha.

An samu guraben karatun ne a kasar India, Sudan, Cyprus, China da sauransu.

Hukumar daukar nauyin karatun ta jihar Zamfara din ta tantance daliban da suka samu nasara. A cikinsu kuwa wasu na kasashe daban-daban sun fara tafiya karatunsu.

Sakamakon barkewar muguwar cutar coronavirus, daliban da aka yankewa tafiya kasar China ana dakatar da tafiyarsu.

Mai bayar da shawara na musamman ga gwamna Matawalle a kan lamurran daukar dawainiyar karatu, Lukman Majidadi, wanda ya tabbatarwa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya wannan cigaban, ya ce an yi hakan ne don kariya ga rayukan matasan maza da mata.

“Don kariya ga daliban Najeriyan da kasar baki daya, mun yanke hukuncin soke tafiyar matasa 20 da suka samu guraben karatu a kasar China din. A halin yanzu muna kokarin samar musu da guraben karatu a wasu kasashen da ke lafiya. Mun sanar da daliban da abin ya shafa tare da kiran su a kan kada su damu tunda gwamnan ya basu damar. Umarni ne kuma za a tura su makaranta,” Lukman ya tabbatar.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa ana tsammanin daliban za su karanci fannin likitanci, na’ura mai kwakwalwa, zane da kimiyyar gine-gine da sauransu.

Coronavirus: Gwamnatin jihar Zamfara ta fasa kai dalibai 20 karatu a China
Coronavirus: Gwamnatin jihar Zamfara ta fasa kai dalibai 20 karatu a China
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Masu binciken kimiyya a kasar Isra'ila sun gano riga-kafin Coronavirus

A ranar Alhamis ne aka fara samun mai cutar coronavirus a Najeriya. Kamar yadda bincike ya nuna, dan asallin kasar Italiya ne wanda ya je hutu kasarsa sannan ya dawo Najeriya inda yake aiki a matsayin Injiniya a jihar Legas.

Wasu disassun hotunan dan kasar Italiya da aka kebe a asibitin jihar Legas a kan cutar Coronavirus sun bayyana. Kwamishinan lafiyar jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi ne ya wallafa hotunan a shafinsa.

Farfesa Abayomi ya ziyarci mutumin da aka kebe din inda ya wallafa hotunan ziyarar a shafinsa na tuwita. Kamar yadda ya walllafa, “Na ziyarci mara lafiyar da ke dauke da cutar COVID-19 a asibiti inda jami’an kiwon lafiya ke kula da shi. Na yi magana da shi tare da tabbatar masa da cewa gwamnatin jihar Legas ta shirya tsaf don shawo kan matsalarsa.”

“A yayin da na ziyarci asibitin, na yi amfani da damar wajen zagaya asibitin da kuma ganin gyaran da aka yi a dakunan. A nan da kwanaki kadan za a kammala gyaran. Na gamsu da gyaran tare da kokarin asibitin,” ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel