Yanzu-yanzu: Masu binciken kimiyya a kasar Isra'ila sun gano riga-kafin Coronavirus

Yanzu-yanzu: Masu binciken kimiyya a kasar Isra'ila sun gano riga-kafin Coronavirus

Wasu masu bnciken kimiyya a cibiyar bincike ta Migal Galilee da ke kasar Isra'ila ta samo riga-kafin cutar coronavirus ta tsuntsaye kuma nan ba da dadewa ba za ta samo riga-kafin cutar ta mutane.

Cutar dai ta yi kamari a dabbobi. Ma'abota binciken sun ce riga-kafin tayi amfani ga dabbobi amma yanzu za a kara gwadata a wajen bincike a kimiyyance.

Bayan shekaru hudu na binciken bangarori da yawa wanda ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Isra'ila ta dau nauyi tare da hadin guiwar ma'aikatar noma da kiwo, MIGAL ta wallafa a shafinta na yanar gizo cewa ta gano riga-kafin mugunyar cutar da ta addabi kasashen duniya da yawa.

Yanzu-yanzu: Masu binciken kimiyya a kasar Isra'ila sun gano riga-kafin Coronavirus
Yanzu-yanzu: Masu binciken kimiyya a kasar Isra'ila sun gano riga-kafin Coronavirus
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Hargitsi tsakanin shugabannin Boko Haram da ISWAP: Akwai yuwuwar Shekau ya sheka lahira

MIGAL ta gano cewa, akwai babbar kamanceceniya tsakanin cutar Covid-19 ta dabbobin da ake kiwatawa tare da ta mutane kuma hanya daya ce ake yada ta. Wannan kuwa ya nuna cewa akwai yuwuwar bayyanar riga-kafin cutar ta mutane nan ba da dadewa ba bayan an fitar da ta tsuntsayen.

"Ganin yadda jama'a ke bukatar riga-kafin cutar Coronavirus da gaggawa, muna yin duk abinda ya dace don ganin mun samota. Muna kokarin ganin mun samo riga-kafin cutar nan da makonni 8 zuwa 10 kuma mu samo hanyar maganceta kwata-kwata na da kwanaki 90," cewar David Zigdon, babban jami'in cibiyar bincike ta MIGAL.

"Wannan zai zama riga-kafi be wanda za a iya sha ta baki yadda kowa zai iya samu. A halin yanzu muna tattaunawa da wasu bangarori ne wadanda za su iya taimakawa wajen karfafa binciken riga-kafin na jama'a tare da kokartawa wajen gano maganin cutar."

Chen Katz, shugaban fasahar da ta shafi jikin dan Adam na MIGAL, ya ce "masu binciken a MIGAL sun gano cewa riga-kafin da za a sha ta baki na mugunyar cutar zai fi kokari wajen shiga duk wani sako da lungu na jikin dan Adam tare da assasa kwayoyin yakar cutar jikin dan Adam yakar cutar da wurwuri."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel