Buhari ya sallami shugaban tsarin yi ma tsaregun Neja Delta afuwa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da mai kula da tsarin gwamnati na yin afuwa ga tsagerun Neja Delta tare da basu tallafim watau Amnesty Programme, kamar yadda fadar shugaban kasa ta bayyana.
Kaakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Juma’a, 28 ga watan Feburairu, inda yace shugaban kasa ya dauki wannan mataki ne biyo bayan korafe korafe da aka yi a kan shugaban Amnesty, Charles Dokubo.
KU KARANTA: Da dumi dumi: Dan kwallon Najeriya ya kamu da cutar Coronavirus

Asali: UGC
“Biyo bayan koke koke da korafe korafe da ofishin mashawarcin shugaban kasa a kan harkar tsaro, NSA, ta samu a kan shugaban tsarin afuwa na gwamnati, shugaban kasa ya umarci NSA ya kafa kwamitin da za ta kula da tsarin.
“Daga cikin ayyukan kwamitin akwai tabbatar da an tafiyar da kudaden gwamnati yadda ya kamata tare da kashe su cikin adalci da gaskiya da gaskiya, tare da la’akari da manufar gwamnati na kawar da matsalolin Neja Delta da yaki da rashawa a tsarin afuwa.
“Don haka NSA ya baiwa shugaban kasa shawarar a dakatar da shugaban tsarin afuwar, Farfesa Charles Quaker Dokubo, kuma tuni shugaban kasa ya amince da wannan shawarar, sallamar ta fara aiki nan take.” Inji sanarwar.
A wani labarin kuma, Babban jami’in hukumar lafiya ta duniya, ta majalisar dinkin duniya, WHO, a Najeriya, Dakta Clement Peter ya jinjina ma namijin kokarin da Najeriya take yi wajen yaki da cutar Coronavirus tun bayan bullarta a Najeriya.
Peter ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja, a cikin ma’aikatar kiwon lafiya, inda yace abin a yaba ne yadda Najeriya ta yi gaggawar gano cutar a Legas, kuma tana kula da shi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng