Atiku ya bawa gwamnatin Buhari shawara kan yadda za ta magance Coronavirus

Atiku ya bawa gwamnatin Buhari shawara kan yadda za ta magance Coronavirus

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya shawarci gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari shawara ta mayar da hankali tare da zage damtse wurin daukan mataki kan Coronavirus.

An samu bullar cutar na farko ne a jihar Legas a ranar Alhamis, yayin da an samu bullar cutar a wasu kasashen duniya 12 cikin sa'o'i 48.

A sanarwar da ya fitar a ranar Juma'a, Atiku ya ce ya zama dole Najeriya ta dauki matakai irin wadanda ta dauka yayin bullar cutar Ebola.

Ya ce, "Ya zama dole mu tuna yadda muka yaki Ebola inda muka zama kasa na farko a duniya da ta ci galaba a kan mummunar cutar a shekarar 2014. Yaya Najeriya ta cimma wannan nasarar? Mun cimma nasarar ne ta hanyar hadin kai.

"Ya zama dole gwamnati mai ci yanzu ta yi aiki tare da gwamnatocin jihohin Legas da Rivers. An samu cikakken hadin kai da aiki tare wadda hakan ne ya bayar da damar cin galaba a kan cutar mai kisa."

DUBA WANNAN: Hargitsi tsakanin shugabannin Boko Haram da ISWAP: Akwai yuwuwar Shekau ya sheka lahira

Wazirin Adamawan ya kuma bayar da shawarar cewa yanzu ba lokaci bane na nuna dan yatsa.

Atiku ya bayyana cewa Najeriya na bukatar daukan matakai kwarara domin kare afkuwar yaduwar cutar.

"A baya-bayannan, mun rufe iyakokin kasar mu saboda kare tabarbarewar tattali arziki. Yanzu lokaci ne da za a dakatar da jirage masu tashi da shigowa kasar duba da yaduwar da cutar ke yi.

"Dan takarar shugaban kasar na PDP a shekarar 2019 ya kuma shawarci a samar da na'urorin gwajin cutar a filayen jiragen saman mu.

"Abinda ya fi muhimmanci, kada 'yan Najeriya su firgita. Al'umma da gwamnati duk sun hada kai sun kawar da Ebola a baya, kuma yanzu shima za mu iya kawar da wannan annobar," in ji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel