Dalilin da yasa ba zan iya kaddamar da Shari'a ba idan aka zabe ni shugaban kasa - Yarima
Tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma Sanata tarayyar Najeriya, Sanata Ahmed Sani Yarima ya ce ba shi da wata shiri na kaddamar da shari'ar musulunci a dokar Najeriya idan an zabe shi a matsayin shugaban kasa a 2023.
Yarima yana shirin fitowa takarar kujerar shugabancin kasa a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Da ya ke magana a wata hira da ya yi da Daily Trust a gidansa da ke Abuja, Yarima ya ce: "Na kaddamar da shari'ar ne a karkashin dokar Najeriya."

Asali: UGC
DUBA WANNAN: Yadda wata mata ta mutu bayan kammala zina da saurayinta dan sanda
"Na shirya kudirin doka kuma na aike wa majalisar jiha kuma majalisar ta amince ta aiwatar da shi ya zama doka saboda jihar mu galibi al'umma ne masu addini iri daya kuma na tuntubi Kirista a jihar.
"Na yi taro da Kungiyar Kirista ta Najeriya (CAN) reshen jihar Zamfara kuma mun fahimci juna cewa dokar kawai musulmi za ta shafa.
"Ni musulmi ne kuma ina son in rayu in kuma mutu a matsayin musulmi. Ina son yin addini na kamar yadda dokar kasa ta bani dama. Mutane ba su fahimci batun shari'a bane. Babu tilas a addini.
"Kundin tsarin mulkin Najeriya ce ake amfani da ita kuma abinda zan fada wa mutane kenan. Na kasance a majalisar dattawa da hakan na ke so da na gabatar da dokar kafa shari'a amma na san ba zai yiwu ba. Dama can akwai shari'a a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya. Abinda na yi kawai shine aiwatar da shari'ar a matakin jiha. Babu bukatar in ce zan aiwatar da shari'a a matakin kasa, ba zai yiwu ba."
Sai dai Yarima ya ce idan har zai iya gamsar da Majalisar Tarayya ta amince da dokar, zai iya kaddamar da shari'a a matakin kasa.
Ya kara da cewa, "A matakin kasa, muna da majalisar wakilai da majalisar dattijai, idan na aike da kudirin aiwatar da shari'a kuma suka amince da shi, shikenan sai a aiwatar."
Tsohon gwamnan ya ce ya shiga wata makarantar kasa da kasa na koyon larabci a wani kwas da ya ke yi a kan addinin musulunci domin ya kara zurfafa fahimtarsa a addinin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng