Da dumi dumi: Dan kwallon Najeriya ya kamu da cutar Coronavirus

Da dumi dumi: Dan kwallon Najeriya ya kamu da cutar Coronavirus

Matashin dan kwallon Najeriya dake taka leda a kasar Italiya, mai suna King Paul Akpan Udoh ya kamu da mugunyar cutar nan ta Coronavirus wanda a yanzu haka ta zama annoba a duniya gaba daya.

Jaridar TheCables ta ruwaito Paul ne da kwallo na farko daya fara kamuwa da wannan cuta. Paul dai yana kwallo ne a kungiyar Piannes a rukunin C na hukumar kwallon kafa ta Italiya.

KU KARANTA: Jerin bayanai 11 da ba su inganta ba dangane da cutar Coronavirus

Da dumi dumi: Dan kwallon Najeriya ya kamu da cutar Coronavirus
Da dumi dumi: Dan kwallon Najeriya ya kamu da cutar Coronavirus
Asali: Facebook

A ranar 27 ga watan Feburairu aka fara gano cutar a tattare da shi, kuma tun daga nan aka kebance shi daga jama’a. shi dai Paul mai shekaru 22 ya fara kwallonsa ne a kungiyar Reggiana, daga nan ya koma Juventus a shekarar 2011, inda suka sake mayar da shi Regianna.

Baya Regianna, Paul ya sake komawa Juventus, amma bai dade ba ya wuce Virtus Lanciano a matsayin dan kwallon aro a shekarar 2016, ya sake komawa Juventus, su ma suka sake mika shi aro zuwa Pontedera, bayan taka leka a wasu kungiyoyi 3, Paul ya koma Pianesa a shekarar 2019.

Ita dai wannan cuta da aka fara samunta daga birnin Wuhan na kasar China tana shafar numfashin dan Adam ne, kuma zuwa yanzu sama da mutane 80,000 sun kamu yayin da akalla mutane 2,000 suka mutu, yawancinsu a kasar China.

A wani labarin kuma, Babban jami’in hukumar lafiya ta duniya, ta majalisar dinkin duniya, WHO, a Najeriya, Dakta Clement Peter ya jinjina ma namijin kokarin da Najeriya take yi wajen yaki da cutar Coronavirus tun bayan bullarta a Najeriya.

Peter ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a babban birnin tarayya Abuja, a cikin ma’aikatar kiwon lafiya, inda yace abin a yaba ne yadda Najeriya ta yi gaggawar gano cutar a Legas, kuma tana kula da shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel