Nigeria zata kawar da Coronavirus kamar yadda ta kawar da Ebola - NCDC

Nigeria zata kawar da Coronavirus kamar yadda ta kawar da Ebola - NCDC

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Nigeria NCDC ta samar da jamian da zasu taimakawa gwamnatin Jihar Legas, waajen dakila bullar coronavirus ta farko a Nigeria.

Darakta Janar na Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Nigeria, Dr Chikwe Ihekweazu, ya bayyanawa manema labarai hakan ne a Abuja.

Ihekweazu yace wajibi ne asibitoci su lura sosai su zauna cikin shiri.

Ya laburta cewa: “Cibiyar zata cigaba da sanar da yan Nigeria halin da ake ciki. Yana da muhimmanci dasu mayar da akan al’amarin kuma su cira tsoro."

“Yan Nigeria su kare kansu, su kwantar da hakalinsu sannan su rika shan ruwa da yawa”.

Yace yan Nigeria su yawaita wanke hannu, su kauracewa sa hannu a ido, baki da hanci, Sannan idan wani ya kamu da zazzabi, tari, da nishi da kyar, ya garzaya asibiti da wurwuri.

Ya tabbatarwa Yan Nigeria cewa yin haka zai sa a kawar da cutar coronavirus kamar yadda aka kawar da Ebola.

Nigeria zata kawar da Coronavirus kamar yadda ta kawar da Ebola - NCDC
Nigeria zata kawar da Coronavirus kamar yadda ta kawar da Ebola - NCDC
Asali: Twitter

DUBA NAN Jerin bayanai 11 da ba su inganta ba dangane da cutar Coronavirus

A bangare guda, Sabbin bayanai sun bayyana cewa dan italiyan da ke dauke da cutar Coronavirus ya ziyarci jahar Ogun kafin a kai shi Lagas inda aka tabbatar da cewar yana dauke da cutar.

An tattaro cewa Dan kasar Italiyan, wanda ya shigo Najeriya ta jirgin Turkiyya, ya nuna alamun cutar a jahar Ogun kafin aka yi gaggawan kais hi Lagas domin yin bincike a tsanaki a cibiyar kula da cututtuka ta Najeriya a Yaba.

Da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnati Marina, Gwamna Babajide Sanwo-Olu tare da kwamishinan lafiya na jahar, Farfesa Akin Abayomi ya bayyana cewa mutumin bai nuna kowani alama na cutar Coronavirus ba da farko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel