Abubuwa 7 da ya kamata mutane su yi bayan bullar Coronavirus a Najeriya

Abubuwa 7 da ya kamata mutane su yi bayan bullar Coronavirus a Najeriya

A ranar Alhamis ne gwamnatin jihar Legas da ma'akatar lafiya ta tarayya suka tabbatar da bullar kwayar cutar Coronavirus (COVID-19) a Najeriya.

An samu kwayar cutar ne a jikin wani dan kasar Italiya da ya ziyarci Legas domin yin kasuwanci. Tuni dai an kebe shi kuma yana karbar magani a asibitin cututuka masu yaduwa da sauri a Yaba, Legas.

Ga wasu abubuwa bakwai da ya dace 'yan Najeriya su yi bayan bullar cutar da Coronavirus a Najeriya kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Abubuwa 7 da ya kamata mutane su yi bayan bullar Coronavirus a Najeriya
Abubuwa 7 da ya kamata mutane su yi bayan bullar Coronavirus a Najeriya
Asali: Twitter

1. Kada a firgita

Abu na farko da ya dace mutane su sani shine babu bukatar a firgita. Irin wannan cututtukar su kan kara yaduwa ne lokacin da mutane suke cikin firgici domin a lokacin ne mutane suka fi yi kuskure.

Babu bukatar a firgita domin kimanin mutane 30,000 da suka kamu da cutar sun warke a shekarar 2020 kawai.

Najeriya ta fuskanci Ebola ya kuma yi nasara a kan shi duk da cewa Ebola ya fi Coronavirus hadari.

2. Wanke hannu

Ma'aikatar Lafiya ta Tarayya ta shawarci mutane su rika wanke hannayensu lokaci zuwa lokaci da sabulu da ruwa. Akwai bukatar kuma a rika amfani da sinadarin kawar da kwayoyin cuta wato hand sanitizer wurin wanke hannun.

3. A dena kusantar mutane da ke atishawa ko tari

Mutane su dena kusantar duk wanda ke tari ko atishawa domin suna cikin alamomin cutar. A rika bayar da tazarar kimanin mita daya da rabi ga duk masu wannan alamomin.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce idan mutum ya yi atishawa ko tari ya kan fitar da kwayoyin cutar daga bakinsa ko hancinsa kuma na kusa da shi suna iya shaka.

4. A guji wuraren cinkoso

Mutanen da ke tari ko atishawa su guji zuwa wuraren da akwai cinkoson mutane, su zaune a gida ko kuma su kebe kansu.

Duk da cewa abu ne mai wuya ya kamata mutane su guji wurin da akwai cinkoso. Duk wanda ke tari ko atishawa ya garzaya asibiti don ganin likita.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Wani mutum ya sake fitowa daga mota ya daka tsalle ya fada ruwa a Legas (Hotuna)

5. A kiyaye tsafta

Mutane su rika tsaftace kansu ta hanyar rufe bakinsu da hancinsu da hankici ko tissue paper yayin da suke atishawa ko tari.

Kwayar cutar na yaduwa ne ta iska saboda haka tsafta na iya kiyaye yaduwar ta.

6. Duk wanda ke da alamomin cutar ya zauna a gida

Duk wanda ya lura yana da alamomi da suka hada da zazzabi, tari ko rashin iya numfashi sosai ya kira wadannan layukan wayan a jihar Legas 08023169485, 08033565529 ko 08052817243.

Kana kuma iya kiran wannan layin a kyauta ko dare ko rana 0800-970000-10.

7. Ku cigaba da bibiyar labarai game da cutar

Ya dace mutane su cigaba da bibiyar sahihan kafafen watsa labarai domin sanin halin da ake ciki game da cutar. Wasu daga cikin kafafen sun hada da ma'aikatar lafiya ta kasa, ma'aikatar lafiya ta jihar Legas da kuma NCDC.

Ana iya yi wa mutum maganin Coronavirus idan ya sanar da mahukunta da zarar ya ga alamomin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel