Iran ta fadi hukuncin da za a yi wa masu yada labaran karya kan Coronavirus

Iran ta fadi hukuncin da za a yi wa masu yada labaran karya kan Coronavirus

Gwamnatin kasar Iran ta yi barazanar yi wa duk wanda aka kama yana yada labaran karya a kan cutar Coronavirus bulala tare da aike wa da shi gidan yari. Cutar a halin yanzu ya kashe mutane 26 a Iran.

Mai magana da yawun kwamitin shari'a na majalisar kasar, Hassan Norouzi ya ce duk wanda aka samu yana yada karya zai fuskanci hukuncin shekaru uku a gidan yari tare da bulala kamar yadda shari'a ta tanada.

Jaridar Tehran Times ta ruwaito cewa Norouzi ya ce, "Yada labaran karya a kan Coronavirus zai janye fargaba tsakanin mutane. Hakan kuma zai iya janyo abubuwa su tabarbare a kasar."

Iran ta fadi hukuncin da za a yi wa masu yada labaran karya kan Coronavirus
Iran ta fadi hukuncin da za a yi wa masu yada labaran karya kan Coronavirus
Asali: Twitter

Nourouzi ya kara da cewa a halin yanzu an kama mutane 24 suna yada jita-jita a kan kwayar cutar kuma za su fuskanci hukuncin da Shari'a ta tanada.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Wani mutum ya sake daka tsalle ya fada ruwa a Legas (Hotuna)

A wani rahoton, Iran ta tabatar da mutuwar mutane bakwai sakamakon kamuwa da cutar ta Coronavirus cikin sa'o'i 24 a jiya wadda hakan na nuna cewa adadin wadanda suka mutu ya kai 26 wadda shine mafi yawa bayan wadanda suka mutu a China.

An kuma tabbatar cewa wasu karin mutane 106 sun kamu da cutar wadda hakan na nuna cewa jimlar wanda suka kamu da cutar ya kai 245 a kamar yadda mai magana da yawun hukumar Kianoush Jahanpour ya fadi yayin taron majalisar gwamnatin kasar.

Kazalika, a karo na farko an samu bullar kwayar cutar na Coronavirus a Legas Nigeria.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel