Buhari ya yi wa Sarki Sanusi II ta'aziyar rasuwar kawunsa

Buhari ya yi wa Sarki Sanusi II ta'aziyar rasuwar kawunsa

Ambasada Ado Sanusi, Dan Iyan Kano kuma kawu ga mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya rasu.

Shugaba Muhammadu Buhari a jiya ya mika sakon ta'aziyya ga Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II bisa rasuwar kawunansa, Ambasada Ado Sanusi, Dan Iyan Kano.

Buhari, cikin sanarwar da mai magana da yawunsa Garba Shehu ya fitar ya bayyana bakin cikinsa bisa rasuwar Ambasaddan.

Buhari ya yi wa Sarki Sanusi II ta'aziyar rasuwar kawunsa
Buhari ya yi wa Sarki Sanusi II ta'aziyar rasuwar kawunsa
Asali: Twitter

Ya kuma mika saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin, Gwamnatin jihar Kano da mutanen jihar baki ɗaya a kan abinda ya kira "babban rashi na dattijo mai nagarta kuma ma'aikacin gwamanti da ya yi aiki tuƙuru."

"Ya bayyana marigayin a matsayin wakili na gari kuma uban ƙasa da ya yi ƙasarsa da garinsa hidima yadda ya dace."

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Wani mutum ya sake fito wa daga mota ya daka tsalle ya fada ruwa a Legas (Hotuna)

A mun kawo muku cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da yasa bai tsoma baki ba cikin rikicin da ke faruwa a jihar ta Kano tsakanin gwamnan jihar da Sarki Sanusi II.

An ruwaito cewa shugaban kasar ya ce dalilin da yasa bai tsoma baki ba a cikin lamarin shine saboda batun na gaban kotu.

Shugabba Muhammadu Buhari ya yi wannan jawabin ne yayin ganawarsa da gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje yayin murnar rantsar da sabbin zababbun 'yan majalisar tarayya daga jihar.

A wani rahoton, Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar ya ce almajirai ba miyagu bane ko bata gari kamar yadda wasu ke tunani, ya kara da cewa kawai sun tsinci kansu ne a mawuyancin hali.

Sa'ad Abubakar ya yi wannan jawabin ne yayin wani taro na murnar cika shekaru 50 da kafa asusun ilimi ta musulunci (IET).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel