Gwamnatin Kano za ta dauki matasa 2,200 don aikin samar da tsaro

Gwamnatin Kano za ta dauki matasa 2,200 don aikin samar da tsaro

Gwamnan jahar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa jahar Kano ta kammala shirin daukan sabbin jami’an tsaro guda 2,200 domin taimaka ma hukumomin tsaro dake jahar wajen samar da ingantaccen tsaro.

Premium Times ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Abba Anwar a ranar Alhamis, wanda ya bayyana cewa za’a dauki matasan ne daga kananan hukumomin jahar 44, inda kowacce karamar hukumar za ta samu jami’ai 50.

KU KARANTA: A halin yanzu Iyalaina sun barbazu a gidajen yan uwana suna rabe rabe – Buba Galadima

Anwar yace Ganduje ya bayyana haka ne a yayin sanya tubalin ginin cibiyar horas da jami’an Sojojin Najeriya a dajin Falgore ake karamar hukumar Tudun Wada ta jahar Kano, inda yace sun kirkiri wannan tsarin hada jama’an gari da jami’an tsaro ne don inganta tsaro.

Sai dai Ganduje ya ce hukumomin tsaro na gwamnati ne zasu baiwa wadannan matasa horo, su nuna musu yadda ake aiki, sa’annan kuma su zasu sanya musu ido a ayyukan da zasu gudanar.

A hannu guda kuma, gwamnatin jahar ta baiwa rundunar Sojin Najeriya kimanin eka 2,169 domin gidan cibiyar bayar da horo ga jami’an Soji a cikin dajin Falgore, cibiyar za ta kunshi dakin taro, dakin cin abinci, dakunan hasoshin Soji da kananan Soji da kuma sashin koyon harbi, asibiti da dakin baki.

Haka zalika gwamnatin za ta gina labar dabbobi don amfani Fulani makiyaya kamar yadda gwamnatin tarayya ta kudiri aniya domin rage aukuwar rikici tsakanin makiyaya da manoma.

A jawabinsa, Ministan tsaro, Bashir Magashi yay aba da kokarin da gwamnatin jahar Kano ta ke yi wajen inganta tsaro a jahar, inda yace ayyukan zasu inganta tattalin arzikin jahar da ma na makwabtansa.

Haka zalika Magashi ya gode ma shugaban kasa Muhammadu Buhari daya bayar da yanayi mai kyau na gudanar da ayyukan. Daga cikin wanda suka halarci taron akwai wakilin babban hafsan Sojan kasa, kwamandan rundunar ta 1, manyan hafoshin Soji da yan siyasa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel