Dan majalisa daga Kano ya roki takwarorinsa su bayar da wani kaso na albashinsu ga hukumomin tsaro

Dan majalisa daga Kano ya roki takwarorinsa su bayar da wani kaso na albashinsu ga hukumomin tsaro

Wasu ‘yan majalisar wakilai na tarayya sun shawarta ranar Alhamis a kan yadda za a kawo tabbataccen tsaro a kasar nan. Bayan tashin wani dan majalisar wakilan daga jihar Kano a karkashin jam’iyyar APC mai suna Nasiru, ya bukaci ‘yan majalisar da su hada wani so na albashinsu don tallafawa hukumomin tsaro a kasar nan.

A taron majalisar na yau Alhamis, dan majalisa Babajimi Benson daga jihar Legas a karkashin jam’iyyar APC, ya mika bukatar mai taken “Hanyar samar da tallafin kudi na musamman, horarwa da kuma samar da kayan tsaro na zamani don farfado da hukumomin tsaron Najeriya, da kuma matsaloli irin wadannan”.

A yayin bada gudumawa a kan tattaunawar, Ali ya ce “Ina bada shawarar cewa kowanne daga cikinmu ya dinga bada gudumawa na wani kaso na albashinsa,”

Ya ce, “Idan aka wadata rundunar sojin Najeriya, zasu yi aiki fiye da yadda suke yi kamar yadda ake gani idan an tura su kwantar da tarzoma a kasashen ketare.”

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, a yayin magana a kan hakan, Sada Solo Jibia daga jihar Katsina kuma dan jam’iyyar APC, ya ce a gaggauta karbar bukatar saboda ba mai wuya ba ce.

Dan majalisa daga Kano ya roki takwarorinsa su bayar da wani kaso na albashinsu ga hukumomin tsaro
Dan majalisa daga Kano ya roki takwarorinsa su bayar da wani kaso na albashinsu ga hukumomin tsaro
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: An fitar da sakamakon gwajin cutar Coronavirus da aka yi wa wani ɗan China a Legas

Ya ce, “Rundunar sojin Najeriya ce matakin tsaronmu na farko. Wannan zai rufe gibin da ke tsakanin rundunar sojin da gwamnatin Najeriya. Idan kuma aka tara kudin, za su yi matukar amfani.”

A wani rahoto na daban, Wani dan majalisar wakilai daga jihar Borno, Ahmadu Jaha ya yi barazanar yin murabus saboda rashin tsaron da ya addabi yankin Arewa maso gabas. A yayin zaman majalisar a ranar Talata, ya yi barazanar yin murabus din ne tare da zargar sojin kasar nan da yin sansanin kare kansu, kamar yadda gidan talabijin din Channels ya ruwaito.

Kamar yadda ya ce, hakan na sa mayakan Boko Haram din su yi ta harar farar hula. Jaha ya kara da cewa sojojin na zaune ne kawai a sansanin, inda suke korar 'yan ta'adda a maimakon yakarsu. Dan majalisar ya jaddada bukatar sallamar shugabannin tsaron kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel