Babu dansandan dake da ikon bincikar wayoyinku – hukumar Yansanda ga yan Najeriya

Babu dansandan dake da ikon bincikar wayoyinku – hukumar Yansanda ga yan Najeriya

Tsohuwar mai magana da yawun rundunar Yansandan jahar Legas, Dolapo Badmus ta bayyana cewa babu wani jami’in Dansanda dake da hurumin binciken wayar salular dan Najeriya, duk wanda ya yi haka ya ci zarafin yan kasa.

Punch ta ruwaito Dolapa ta bayyana haka ne yayin da take tattaunawa da taron murnar makon kafafen sadarwar zamani na shekarar 2020 da aka gudanar a jahar Legas a ranar Laraba, 26 ga watan Feburairu.

KU KARANTA: Badakalar satar naira biliyan 2: Abdulrashid Maina na barazanar kashe direbobinsa

Babu dansandan dake da ikon bincikar wayoyinku – hukumar Yansanda ga yan Najeriya
Dolapo
Asali: Instagram

“Takurar da Yansanda suke ma jama’an Legas suna bincikar wayoyinsu ya zama abin damuwa, bai dace ba kuma wuce gona da iri ne, yin hakan tamkar umartar mutum ya cire wandonsa ne don kawai kana bukatar yin aikin ka.” Inji ta.

A cewar Dolapo, hakan bai kamata ba musamman kasancewar wayar salula mallakin mutum ne, kuma sirrinsa ne, ta kara da cewa wayoyin salula na dauke da bayanan sirrin mutum kamarsu bayanan asusun banki da sauransu.

Sai dai Dolapo ta kawo inda ya zama wajibi yansanda su duba wayar mutum, wannan kuma shi ne “Idan har akwai bukatar gudanar da bincike a kan hakan, sai dai kawai ka san a Najeriya mu ke, kuma har yanzu muna kokarin neman kwarewa a aikin Yansanda ne.”

A wani labarin kuma, tsofaffin direbobin tsohon shugaban kwamitin gudanar da garambawul ga dokokin fansho a Najeriya, Abdulrashid Maida sun koka ga kwamishinan Yansandan jahar Kaduna game da barazana ga rayuwarsu da suka ce Maina da matarsa Laila suke musu.

Direbobin sun hafa da Abdul Ibrahim da Ibrahim Muhammad sun bayyana ma kwamishinan Yansandan Kaduna cewa Maina wanda a yanzu haka yake tsare a kurkukun Kuje yana aika musu da sakon barazanar kisa saboda sun tattauna da jami’an EFCC.

A yanzu haka EFCC na tuhumar Maina da tafka laifuka guda 12 dasuka danganci satar zambar kudi naira biliyan 2. Direbobin sun bayyana cewa bayan EFCC ta kama Maina, sai suma ta kamasu ta yi musu tambayoyi da ya danganci tuhume tuhumen da take yi ma Mainan.

Abdul da Ibrahim sun bayyana cewa bama su kadai ba, Maina da matarsa na amfani da jami’an Yansanda wajen tsoratar da iyalansu tare da barazanar kashesu, don haka suka shiga yar buya don tsira da rayuwarsu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel