Hukuncin kotu: An kashe mayakan kungiyar Boko Haram 10 ta hanyar bude musu wuta

Hukuncin kotu: An kashe mayakan kungiyar Boko Haram 10 ta hanyar bude musu wuta

Dakarun sojojin kasar Chadi sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram guda goma ta hanyar bude mus wuta.

An kashe mayakan ne kwana daya kacal bayan wata kotun kasar da ke birnin N'Djamena ta same su da laifin aikata ta'addanci kamar yadda ake tuhumarsu.

Majiyar jami'an tsaro ta bayyana cewa dakarun sojoji ne suka bude wa mayakan goma wuta a arewacin babban birnin jihar, N'Djemena.

An gurfanar da dukkan mayakan goma ne a kan rawar da suka taka a wani hari da ya zama silar mutuwar mutane 38 a watan Yuni na shekarar 2019. Bayan wata daya da kai harin ne kasar Chad ta gabatar da dokar kisa ga 'yan ta'adda.

"Da safiyar yau (Alhamis) aka kashe su ta hanyar bude musu wuta," kamar yadda majiya ta sanar da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Hukuncin kotu: An kashe mayakan kungiyar Boko Haram 10 ta hanyar bude musu wuta
Mayakan kungiyar Boko Haram 10 da aka kashe ta hanyar bude musu wuta a kasar Chad
Asali: Twitter

Daga cikin 'yan ta'addar da aka kashe akwai Mahamat Mustapha da aka fi sani da 'Bana Fanaye', wanda aka bayyana cewa shine ya kista harin da aka kai na watan Yuni.

DUBA WANNAN: Boko Haram: Rawar da 'yan Najeriya zasu taka wajen kawo karshen ta'addanci - FG

Mayakan Boko Haram sun kai harin ne a kan wani ofishin 'yan sanda da ginin makaranta da ke N'Djamena, lamarin da ya yi sanadiyyar raunata mutane fiye da 100 bayan wadanda suka mutu.

An kara samun fashewar bamabamai a wata kasuwa da ke babban birnin a watan Yuli, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 15.

Hukuncin kotu: An kashe mayakan kungiyar Boko Haram 10 ta hanyar bude musu wuta
Mahamat Mustapha da aka fi sani da 'Bana Fanaye'
Asali: Twitter

Hare haren ne na farko da mayakan kungiyar Boko Haram 'yan Najeriya suka kai kasar Chad, hedikwatar rundunar sojojin hadin gwuiwa.

Babban mai gabatar da kara, Bruno Mahouli Louapambe, ya shaida wa AFP cewa an samu mayakan 10 da laifukan da suka hada da hada baki, kisa, barnatar da dukiya ta hanyar amfani da sinadarai masu fashe wa, mallakar makamai ba bisa ka'ida ba, amfani da miyagun kwayoyi da ke juya tunani da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel