Yanzu-yanzu: Mataimakiyar shugabar kasar Iran ta kamu da cutar Coronavirus

Yanzu-yanzu: Mataimakiyar shugabar kasar Iran ta kamu da cutar Coronavirus

Mataimakiyar shugabar kasar Iran kan harkakokin mata da Iyali, Masoumeh Ebtekar, ta kamu da cutar Coronavirus da ta addabi duniya, jaridar kasar ta ruwaito.

Masoumeh Ebtekar ce mambar majalisar zartarwar kasa ta farko da zai kamu da cutar tun lokacin da ta bulla a Iran.

A yau, shugaban kwamitin harkokin wajen Iran na majalisar dokokin kasar, Mojitaba Zolnour, ya bayyana a wani faifan bidiyo cewa shi ma ya kamu da cutar ta Coronavirus.

Hakazalika wani dan majalisa, Mahmoud Sadeghi da mataimakin ministan kiwon lafiyar kasar, Iraj Harichi, sun tabbata da kamuwa da muguwar cutar.

Bugu da kari, gidan talabijin kasar ta sanar a yau Alhamis cewa babban Malami Hadi Khosroshahi, ya mutu sanadiyar kamuwa da cutar.

Yanzu-yanzu: Mataimakiyar shugabar kasar Iran ta kamu da cutar Coronavirus
Yanzu-yanzu: Mataimakiyar shugabar kasar Iran ta kamu da cutar Coronavirus
Asali: Facebook

A bangare guda, Mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Ajayi Boroffice ta bayyana cewa babu abinda akeyi domin kare Najeriya da annobar cutar Coronavirus.

Yayinda yake magana a zauren majalisar yau Alhamis, Sanata Boroffice yace yayinda ya dira babban filin jirgin saman kasa da kasa na Abuja daga kasar Afrika ta kudu ranar Laraba, bai ga ana duba masu shiga kasar ba.

Ya ce innama yar takarda ake baiwa mutane su rubuta ko suna da lafiya ko basu da lafiya. Ya kara da cewa a kasar Afrika ta kudu da yaje, sai da aka tantancesu kafin sauka daga cikin jirgin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel