Boko Haram: Yadda 'yan Najeriya za su kawo karshen rashin tsaro - FG

Boko Haram: Yadda 'yan Najeriya za su kawo karshen rashin tsaro - FG

Sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha, ya ce sai 'yan Najeriya sun bawa koyarwar addini, al'ada da tarbiya muhimmanci sannan za a kawo karshen hare-haren 'yan ta'adda da rashin tsaro a sassan kasa.

Mustapha, wanda Dakta Amina Shamaki, babbar sakatariya a ofishinsa ta wakilta, ya bayyana hakan ne a wurin wani taron harkokin kasuwanci (LCCI) da ya halarta a jihar Legas.

Ya bayyana cewa rashin aiki ne tushen rashin tsaron da ake fama da shi, tare da yin roko ga hukumomin duniya da su taimaka wa gwamnati wajen samar wa da matasa aiki, kamar yadda jaridar 'The Nation' ta wallafa cewa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

Sakataren gwamnatin ya bukaci 'yan Najeriya su kasance masu daukan dawainiyar yaran da suka haifa tare da basu tarbiyar da zata sa su kasance mutane nagari da zasu taimaka wa kasa ta samu cigaba.

"Bukatar kawo karshen rashin tsaro ta shafi kowa da kowa, akwai bukatar gaba dayanmu mu hada kai.

Boko Haram: Yadda 'yan Najeriya za su kawo karshen rashin tsaro - FG
Boss Mustapha
Asali: Depositphotos

"Kowanne mutum yana da rawar da zai taka wajen kawo karshen matsalolin tsaro, mutum zai iya taimaka wa koda da muhimmin bayani ne ko kuma ya yi amfani da karfinsa.

DUBA WANNAN: IGP ya bayar da umarnin rufe ofisoshin rundunar SARS a fadin Najeriya

"Dole mu bawa koyarwar addini, al'adu, da tarbiya muhimmanci domin ta haka ne kawai zamu iya gina al'umma ta gari da kowa zai kasance yana yin abinda ya dace.

"Idan zamu yi hakan, zai kasance muna da mutane masu tarbiya da tsoron Allah, hakan kuma zai saukaka yaki da rashin tsaro, cikin sauki za a samu galaba a kan ta'addanci," a cewarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel