Kawo yanzu, Yan Najeriya 118 suka mutu sakamakon zazzabin ciwon Lassa - NCDC

Kawo yanzu, Yan Najeriya 118 suka mutu sakamakon zazzabin ciwon Lassa - NCDC

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta bayyana cewa adadin yan Najeriya da suka mutu sakamakon zazzabin Lassa ya kai 118.

Tsakanin 1 ga Junairu da 23 ga Febrairu, an gwada mutane 2,633, kuma an tabbatar da 689 daga cikin sun kamu da cutar.

Adadin ya yi tashi gwauron zabo fiye da abinda aka samu a shekarar 2019 inda aka gwada mutane 1,249, aka tabbatar da 381 sun kamu kuma 83 cikinsu suka mutu.

Cutar Lassa ta zama kayar baya a kasar nan kuma kullun kara yaduwa takeyi. Mutane sun fi kamuwa da cutar lokacin bazara, misali tsakanin Nuwamba da Mayu.

A jawabin da cibiyar ta sai a wannan makon, an samun karin mutane 115 da suka kamu da cutar bayan 102 da suka kamu a makon da ya gabata.

An samu ne a jihohin – Ondo, Ebonyi, Edo, Bauchi, Plateau, Benue, Lagos, Enugu, Gombe, Kaduna, Katsina, Kogi, Sokoto, Taraba, Delta, Rivers, Adamawa da Nasarawa.

Hakazalika maaikatan asibiti hudu sun sake kamuwa a jihar Edo da Ondo.

Kawo yanzu, Yan Najeriya 118 suka mutu sakamakon zazzabin ciwon Lassa - NCDC
Kawo yanzu, Yan Najeriya 118 suka mutu sakamakon zazzabin ciwon Lassa - NCDC
Asali: UGC

Kawo yanzu, jihohi 27 ne aka samu bullar cutar Lassa yayinda jihohin Edo, Ondo da Ebonyi suka fi ko ina yawa.

Ainihin dabbar da ke dauke da cutar itace bera. Dan Adam na iya kamuwa da cutar sakamakon cin bera kon cin abincin da bera mai dauke cutar yayi fitsari ciki.

Hakazalika mutum na iya kamuwa da cutar sakamakon hada gumin jiki ko jini da mai dauke da cutar.

Daga cikin alamomin da akan gane mutum ya kamu sune zazzabi, ciwon kai, kasalar jiki, tari, amai da gudawa, zafin kirji. Idan yayi tsananin mutum zai fara zubar da jini ta kunne, hanci, ido, baki, farji, dubura da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel