Yanzu-yanzu: An fitar da sakamakon gwajin cutar Coronavirus da aka yi wa wani ɗan China a Legas

Yanzu-yanzu: An fitar da sakamakon gwajin cutar Coronavirus da aka yi wa wani ɗan China a Legas

Gwamnatin jihar Legas ta tabbatar cewa ɗan asalin ƙasar China da aka kai asibitin Reddington a Ikeja a ranar Laraba an kan zargin ya kamu da cutar Coronavirus baya dauke da ƙwayar cutar.

Kwamishinan Lafiya, Farfesa Aikin Abayomi ne ya sanar da hakan a yayin taron manema labarai a ranar Alhamis inda ya kara da cewa sakamakon gwaje-gwajen ya nuna cewa baya dauke da ƙwayar cutar saboda haka kawo yanzu babu bullar cutar a jihar Legas.

"Ina son in tabbatar wa mutanen Legas cewa muna saka idanu sosai kuma muna kara daukan matakan da suka dace domin kiyaye lafiyar mutanen jihar," in ji shi.

Yanzu-yanzu: An fitar da sakamakon gwajin cutar Coronavirus da aka yi wa wani ɗan China a Legas
Yanzu-yanzu: An fitar da sakamakon gwajin cutar Coronavirus da aka yi wa wani ɗan China a Legas
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tubabbun 'yan Boko Haram daga Nijar sun isa Maiduguri

Yayin da ya ke bayar da cikaken bayani a kan binciken, Abayomi ya bayyana cewa "An sanar da ma'aikatar lafiya game da zargin da ake yi na cewa wani yana dauke da kwayar cutar Coronavirus a asibitin Reddington da ke Ikeja amma binciken da muka gudanar ya nuna cewa mutumin dan asalin China da ya iso Najeriya makonni bakwai da suka gabata da aka kai asibitinn Reddington ya ce yana fama da zazzabi a ranar Laraba."

Asibitin sun bi shawarar da muka basu inda suka kebe mara lafiyar sannan suka sanar da ma'aikatan Lafiya.

"Mun karbi mara lafiyar muka mika shi zuwa wurin kebe marasa lafiya na musamman a asibitin Mainland wadda shine asibitin mu na kwararru. An diba jininsa an kai dakin gwaji na kwayoyin cuta kuma sakamako ya nuna ba ya dauke da kwayar cutar."

Abayomi ya janyo hankulan al'umma su guji wallafa labaran da ba su tabbatar da sahihancinsu ba da ka iya janyo tashin hankali a cikin al'umma ya kuma shawarci mazauna jihar su yi watsi da duk wani labari da bai fito daga bakin ma'aikatan lafiyar ba ko ofishinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel