Saudiyya ta hana shiga Makkah da Madina saboda Coronavirus
Mahukunta a kasar Saudiyya sun hana maniyatta aikin hajji da Umrah shiga Makkah da Madinah domin gudun yada cutar Coronavirus da ke bazuwa a kasashen duniya.
Ma'aikatar harkokin kasashen waje ta Saudiyya ta ƙara da cewa za ta hana baki daga ƙasashen da aka tabbatar da bullar cutar ko inda ta ke barazana ga kiwon lafiyar mutane kamar yadda Bbc ta ruwaito.
Har ila yau, ma'aikatar a shafin ta na Twitter ta kuma ce da dakatar da amfani da shedar katin ɗan kasa a madadin fasfo a lokacin shiga da fita kasar ta Saudiyya.
DUBA WANNAN: Tubabbun 'yan Boko Haram daga Nijar sun isa Maiduguri
A baya mun kawo muku cewa an samu barkewar cutar ta coronavirus karo na farko a nahiyar Afirka. Ministan kiwon lafiya na kasar Algeria ne ya sanar da cewa an samu mutum na farko mai dauke da mummunar cutar a kasar.
Shamsuddin Shito, ministan lafiya na kasar Algeria ya sanar da cewa an samu mai cutar sakamakon tsananin binciken da aka saka a kan tudu da ruwa da kuma duk wata hanyar shiga kasa.
Ya bayyana cewa wani dan asalin kasar Itali ne wanda ya isa kasar a ranar 17 ga watan Fabrairu ke dauke da cutar. An kuma ware mutumin don bashi magani da kulawar da ta dace.
Ya yi kira ga ‘yan kasar Algeria da su kiyaye duk wani bayani da zasu yada a yanar gizo a kan cutar.
Cutar dai ta fara bulla ne a birnin Wuhan da ke kasar China inda a halin yanzu ta shafi mutane 80,000 a duniya tare da kashe 2,700.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://facebook.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng