Badakalar satar naira biliyan 2: Abdulrashid Maina na barazanar kashe direbobinsa

Badakalar satar naira biliyan 2: Abdulrashid Maina na barazanar kashe direbobinsa

Tsofaffun direbobin tsohon shugaban kwamitin gudanar da garambawul ga dokokin fansho a Najeriya, Abdulrashid Maida sun koka ga kwamishinan Yansandan jahar Kaduna game da barazana ga rayuwarsu da suka ce Maina da matarsa Laila suke musu.

Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito direbobin sun hafa da Abdul Ibrahim da Ibrahim Muhammad sun bayyana ma kwamishinan Yansandan Kaduna cewa Maina wanda a yanzu haka yake tsare a kurkukun Kuje yana aika musu da sakon barazanar kisa saboda sun tattauna da jami’an EFCC.

KU KARANTA: Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya ya rasu yana da shekaru 112

Badakalar satar naira biliyan 2: Abdulrashid Maina na barazanar kashe direbobinsa
Badakalar satar naira biliyan 2: Abdulrashid Maina na barazanar kashe direbobinsa
Asali: Facebook

A yanzu haka EFCC na tuhumar Maina da tafka laifuka guda 12 dasuka danganci satar zambar kudi naira biliyan 2. Direbobin sun bayyana cewa bayan EFCC ta kama Maina, sai suma ta kamasu ta yi musu tambayoyi da ya danganci tuhume tuhumen da take yi ma Mainan.

Abdul da Ibrahim sun bayyana cewa bama su kadai ba, Maina da matarsa na amfani da jami’an Yansanda wajen tsoratar da iyalansu tare da barazanar kashesu, don haka suka shiga yar buya don tsira da rayuwarsu.

Lauyansu yace: “Bayan EFCC ta sakesu, sai suka fara samun sakonnin barazana iri iri da cin mutunci, a watan Disambar 2019 matar Maina ta kira Ibrahim inda ta yi masa barazana tare da daukan mataki akansa saboda ya munafuncesu ya nuna ma EFCC motocin Maina da kadarorinsa.

“A ranar 24 ga watan Janairun 2020 da misalin karfe 11 na dare an sake kiran Ibrahim da boyayyen lamba aka yi barazanar kashe shi a duk inda aka same shi, a ranar 27 ga watan ma haka, da misalin karfe 7 na dare mai tsaron Maina ya tafi gidan Ibrahim yana tambayar inda ya shiga.

“Dukkanin masu karar suna cikin fargaba da tsoro, don haka muke kira ka bincike lamarin don kama wadanda ake zargi tare da tabbatar da adalci.” Inji shi.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga manyan hafsoshin tsaron Najeriya da su samar da gudanar da cikakken nazari game da tsare tsare da dabarun da suke amfani dasu a yaki da ISWAP, don duba yiwuwar kirkiro sabbin dabaru.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel