Azzalumai a Najeriya sun ki mutuwa - Shugaban marasa rinjaye na Majalisa, Abaribe

Azzalumai a Najeriya sun ki mutuwa - Shugaban marasa rinjaye na Majalisa, Abaribe

Shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Enyinnaya Abaribe ya bayyana bacin ransa kan tsawon rai da azzaluman mutane ke more wa a Najeriya.

Ababribe ya yi wannan jawabi ne yayin wata taro na musamman da aka shirya don karrama marigayi Sanata Ignatius Longjan mai wakiltan Plateau ta Kudu lokacin yana raye.

Ya ce mutanen kirki da dama suna mutuwa a kasar. Ya bayyana Longjan a matsayin "mai wanzar da zaman lafiya kuma mutumin kirki sosai".

Azzalumai a Najeriya sun ki mutuwa - Shugaban marasa rinjaye na Majalisa, Abaribe
Azzalumai a Najeriya sun ki mutuwa - Shugaban marasa rinjaye na Majalisa, Abaribe
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hana bara a Kano: Malaman Tsangaya sun yi zazzafan martani ga Ganduje

Dan majalisar haifafan jihar Abia ya ce;

"Mun yi irin wannan taron kwanaki kadan da suka gabata, wato taron karrama daya daga cikin abokin aikin mu. Tambayar da na ke son yi a nan ita ce, Shugaban Majalisa, Mene ya sa mutanen kirki ne su ke mutuwa?

"Dukkan azzaluman da ke kasar nan, ba su mutuwa. Mutanen kirki ne su ke mutuwa. Saboda haka a yau, muna yi wa matarsa da 'ya'yansa da mutanen da ya ke wakilta ta'aziyya da ma dukkan 'yan Najeriya."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel