Gwamna Abdullahi Sule ya rattaba hannu a kan dokar hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane

Gwamna Abdullahi Sule ya rattaba hannu a kan dokar hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane

Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya rattaba hannu a kan dokar zartar da hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane a jihar.

"Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta gudanar da mahawara tare da yin duba na tsanaki kafin su amince da dokar.

"Dokar ta ayyana laifuka masu nasaba da garkuwa da mutane da kuma kunshin hukunce-hukuncensu. Daga cikin hukuncin akwai dauri a gidan yari da hukuncin kisa," a cewar gwamnan.

Gwamna Sule ya bayyana cewa gwamnati za ta mallaki duk wata kaddara ta wanda aka samu da laifin garkuwa da mutane.

Kazalika, ya bayyana cewa masu bayar da hayan wurin zama ga masu garkuwa da mutanen, za su iya fuskantar hukuncin daurin shekaru 20 a gidan yari.

Gwamna Abdullahi Sule ya rattaba hannu a kan dokar hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane
Gwamna Abdullahi Sule ya rattaba hannu a kan dokar hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: IGP ya bayar da umarnin rufe ofisoshin rundunar SARS a fadin Najeriya

A wani rahoto na daban, Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule ya haramta bara a titunan jihar. Ya sanar da hakan ne yayin rantsar da hukumar kare hakkin yara a Lafia a ranar Laraba.

Gwamnan ya ce, "ba tare da nuna gadara ba, wannan dokar ta hana bara a tituna kuma ta tanadi hukunci ga iyayen da suka watsar da nauyin da ke kansu. A don haka kuma, gwamnati ta dau matakin saka yaranmu da ke karatu a Tsangaya cikin karatun boko don magance wannan matsalar,"

Gwamna Sule ya ce tabbatar da dokar bada kariya ga yaran za ta tabbatar da tsaro, kiwon lafiyarsu da iliminsu don ci gaban jihar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito. Yayi kira ga shugabannin gargajiya, addinai kuma da jama'a da su goyi bayan wannan salon.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel