Binciken masana: Nan da shekarar 2050 yawan 'yan Najeriya zai kai miliyan 401

Binciken masana: Nan da shekarar 2050 yawan 'yan Najeriya zai kai miliyan 401

- Wani babban masani a fannin tattalin arziki mai suna Wilson Erumebor ya bayyana cewa yawan ‘yan Najeriya zai kai miliyan 401 nan da 2050

- Erumebor ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa a kan soshiyal midiya wanda NESG ta shirya

- Tattaunawar ta kara da tabo fannin zaman lafiya da tsaro mai dorewa da kuma yanayin masana’antu a kasar nan

Wani babban masani a fannin tattalin arziki mai suna Wilson Erumebor ya bayyana cewa yawan ‘yan Najeriya zai yi tashin gwauron zabi inda zai kai kusan miliyan 401 a shekarar 2050.

Erumebor ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa a kan soshiyal midiya wanda NESG ta shirya.

Binciken masana: Nan da shekarar 2050 yawan 'yan Najeriya zai kai miliyan 401
Binciken masana: Nan da shekarar 2050 yawan 'yan Najeriya zai kai miliyan 401
Asali: Facebook

Kamar yadda kwararren ya sanar, wannan yawan da za a yi zai kawo illa ga ababen more rayuwa, ilimi, lafiya da kuma tsaron abinci na kasar nan.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa wannan tattaunawar da aka yi ya dogara ne da sabbin tsare-tsare don taimakawa wajen sauya Najeriya zuwa ta zamani kuma wacce za ta iya gogaggaya da kowacce kasa nan da 2050.

Tattaunawar ta kara da tabo fannin zaman lafiya da tsaro mai dorewa da kuma yanayin masana’antu a kasar nan.

KU KARANTA: Na talauce na shiga tashin hankali bayan aurenta - Miji ya kira matarsa da mai farar kafa

A wannan zaman kuwa, ya ce akwai bukatar ‘yan Najeriya ba tare da an dubi shekaru ba a hada kai a zauna don tattaunawa a kan ci gaban kasar nan.

A bangaren shugaban kungiyar Flying Doctors Nigerian, Dr, Ola Brown ta jaddada cewa akwai bukatar Najeriya ta samu ci gaba, don haka ci gaba da zuba hannayen jari da fitar da kayayyakin da ake samu a kasar nan mafita ne.

“Najeriya ba ta da kudin daukar nauyin kasafinta na kudi kuma akwai bukatar tabuka wani abu a fannin,” ta ce.

Hakazalika, babban mai bayar da shawara na musamman ga gwamnan jihar Legas a kan SDG da kuma zuba hannayen jari, solape Hammond ta jaddada cewa akwai bukatar ‘yan Najeriya su zama jakadan arziki ga kasar nan. Ta bayyana cewa hada kai da bangarori masu zaman kan su zai zama mafita.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel