Maza masu mace daya suna rayuwa rabi da rabi ne - Cewar tsohon dan takarar shugaban kasa

Maza masu mace daya suna rayuwa rabi da rabi ne - Cewar tsohon dan takarar shugaban kasa

- Tsohon da takarar shugaban kasan Najeriya a karkashin jam’iyyar APC, Adamu garba ya ce mazan da suke da mace daya basu more ba

- Adamu Garba ya sanar da hakan ne yayin da yake yin wani tsokaci a kan bidiyon wani miji tare da matan shi biyu

- Idan zamu tuna dai, Garba ya taba cewa gara mace ta amsa sunan matar aure a kan a kira ta da gwamnan babban bankin Najeriya

Tsohon dan takarar shugaban kasa, Adamu garba ya ce mazan da ke da mata daya na rayuwa ne a matsayin rabin mutane.

Adamu Garba dai tsohon dan takarar shugaban kasa ne a karkashin jam’iyyar APC wanda ya ce gaskiya maza masu mace daya basu samun yadda ya dace, kuma suna rayuwa ne rabi da rabi, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Ya sanar da hakan ne a martanin wani bidiyo na wani mutum da matanshi ke faranta mishi.

Maza masu mace daya suna rayuwa rabi da rabi ne - Cewar tsohon dan takarar shugaban kasa
Maza masu mace daya suna rayuwa rabi da rabi ne - Cewar tsohon dan takarar shugaban kasa
Asali: UGC

A kasan bidiyon an rubuta, “magidanci da matan shi biyu."

Adamu garba yayi martani a kan bidiyon inda ya rubuta: “Idan ka dage a wajen mace daya a rayuwarka, dan uwana rayuwarka rabi ce kuma baka samun yadda ya dace. Babu abinda ya fi mata biyu ko fiye da haka dadi. Ina kira ga maza, ku daina bin su ta bayan fage, ku fito ku auresu kiri-kiri sai ku samu kwanciyar hankali.”

Sanannen abu ne cewa Adamu Garba na da mata biyu kuma a kwanakin baya ya ce yana fatan ya kara wasu don cike sunnah.

Kamar yadda aka sani, yana yadawa tare da kara wa maza karfin guiwar kara aure duk in ya samu dama. A kwanakin baya kuwa ya yi wani rubutu da ya samu caccaka mai yawa daga ma’abota amfani da kafafen sada zumunta.

Tsohon dan takarar shugaban kasar kuma dan kasuwar, ya bayyana cewa gara mace ta samu a kira ta da matar aure a kan a kira ta da gwamnan babban bankin Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel