Mun lalata kawancen da ke tsakanin Boko Haram da ISWAP - Buratai

Mun lalata kawancen da ke tsakanin Boko Haram da ISWAP - Buratai

- Babban hafsan sojojin kasar Najeriya, Tukur Buratai ya ce sun yi nasarar tarwatsa kawance da ke tsakanin Boko Haram da ISWAP

- Shugaban sojojin ya bayyana cewa hakan babban nasara ce a yakin da rundunar ke yi da ta'addanci a Najeriya

- Tukur Buratai ya shawarci sojojin Najeriya su cigaba da jajircewa wurin ayyukansu domin dacewa da tsare-tsarensa na inganta aikin sojin

Babban hafsan sojojin kasar Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai ya ce rundunar sojin ta raba kawunnan kungiyoyin Boko Haram da na Islamic State of West African Province (ISWAP).

Daily Trust ta ruwaito cewa Buratai ya fadi hakan ne a hedkwatan sojoji a Abuja yayin jawabinsa a wurin taron kwararrun sakatarorin sojoji.

An raba jiha tsakanin Boko Haram da ISWAP - Buratai
An raba jiha tsakanin Boko Haram da ISWAP - Buratai
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An bayyana dalilin da yasa 'yan kungiyar ISWAP suka kashe dan Mohammed Yusuf

Ya ce, "Ina murna domin mun fara samun nasara a yunkurin da muke na raba mummunar alakar da ke tsakanin Islamic State in West Africa Province ISWAP da burbushin 'yan kungiyar Boko Haram da su kayi saura.

"Muna kai madaidaiciyar hanya kuma ba za mu yarda a kawar mana da hankali ba. Saboda haka ya zama dole mu cigaba da bawa dakarun mu kwarin gwiwa tare da basu daman inganta ayyukansu. Ina son tunatar da ku ce cewa tsari na na 2020 shine tabbatar da kwarewa a aikin soji domin dakarun su samu ikon gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

"A hakan ne na ke umurtar dukkan dakarun mu su rungumi wannan tsarin. Ina kira ga kwamandojin mu su cigaba da jajircewa wurin ganin an tabbatar da nasarorin da aka samu a atisayen Operation Lafiya dole."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel