Zaratan Sojojin Najeriya sun hallaka Alkalin Alkalan kungiyar Boko Haram
Dakarun rundunar Sojojin Najeriya sun kashe babban Alkalin kungiyar ta’addanci na Boko Haram, Akalin Alkalai Muhammad Shuwa a yayin wani samame da suka kaddamar a yankin tafkin Chadi.
Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito wani bincike ya tabbatar da mutuwar akalla kwamandojin kungiyar guda 25 a cikin watanni biyu da suka gabata a sakamakon kara kaimi da wajen yaki da ta’addanci da rundunar Soji arewacin tafkin Chadi ta yi.
KU KARANTA: Tsuguni bata kare ba: EFCC ta tasa keyar ‘Mamar Boko Haram’ a kan zambar N42m
Wasu majiyoyi sun bayyana ma jaridar PRNigeria cewa yan ta’adda da daman a ta arcewa zuwa cikin kasashen Chadi, Nijar da Kamaru sakamakon mace mace da ake yawan samu a sansanonin Boko Haram a dalilin bamabamai da suke binnewa a zagaye da sansanonin, musamman bayan harin jiragen Soji.
“Wasu yan kasashen waje guda biyu dake daukan nauyin yan ta’adda sun mutu a yayin harin hadin gwiwa tsakanin jiragen yakin Najeriya da dakarun Sojin kasa a wani sansanin Boko Hara. Yawancin bakin hauren kwamandojin sun tsere, suka bar yan kasa.” Inji shi.
A wani labarin kuma, Hukumar rundunar Sojan sama ta bayyana cewa jiragenta dake yaki da ta’addanci a yankin jahar Borno masu sunan Rattle Snake 3 sun yi aman wuta a kan wasu gine gine da mayakan Boko Haram ke amfani dasu wajen fakewa.
Mai magana da yawun rundunar, Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka a ranar Talata, inda yace jiragen Rattle Snake suna lalata sansanonin tare da kayayyakin aikin Boko Haram a yankunan Garin Malona da Parisu, duk a cikin dajin Sambisa.
Daramola ya ce a ranar 23 da 24 na watan Feburairu ne Sojojin rundunar Sojan sama dake sarrafa jiragen yakin suka tashi sansanonin biyu a cikin yakin da gwamnatin Najeriya ke yi da yan ta’adda karkashin Operation Lafiya Dole a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.
“Mun kai harin ne bayan samun sahihan bayanai dake tabbatar da mayakan Boko Haram da suka kaddamar da hare hare a garin Garkidan jahar Adamawa sun fito ne daga sansanonin a cikin Sambisa
“Wannan ne yasa rundunar Sojan sama ta tura jiragen yakinta don su yi aman wuta a sansanonin tare da lalata dukkanin gine ginen dake cikinsu da kuma kayan aikinsu da makamansu dake jibge a wajen, kuma daga karshe mun hangesu sun kama da wuta duka.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng