An bayyana dalilin da yasa 'yan kungiyar ISWAP suka kashe dan Mohammed Yusuf

An bayyana dalilin da yasa 'yan kungiyar ISWAP suka kashe dan Mohammed Yusuf

A halin yanzu an rikici ya barke a kungiyar Islamic State of West Africa Province (ISWAP), wani sashi na kungiyar Boko Haram.

Wata majiya ta ce an kashe shugaban kungiyar, Ba'a Idrisa, dan tsohon shugaban kungiyar Mohammmed Yusuf.

Rahotannin sun ce an kashe shi ne tare da wasu kwamandojin kungiyar uku.

Majiyar ta shaidawa The Cable cewa an kashe shi ne da sauran kwamandojin a ranar 9 ga wtaan Fabrairu saboda sun gabatar da wata shawara da sauran 'yan kungiyar su ke ganin ba ta dace ba.

Majiyar ta ce, "Idirisa ya fadawa dakarunsa su dena kashe sojoji da suka kama kuma su rika kyautatawa mutanen kauyukan da suka ziyara.

An bayyana dalilin da yasa 'yan kungiyar ISWAP suka kashe dan Mohammed Yusuf
An bayyana dalilin da yasa 'yan kungiyar ISWAP suka kashe dan Mohammed Yusuf
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Ganduje ya haramta wa Almajirai bara a titunan Kano

"Sai dai hakan bai yi wa wasu 'yan kungiyar ta ISWAP dadi ba. Sunyi zargin cewa Idirisa da sauran kwamandojin suna yi wa gwamnati aiki. Daga bisani suka kashe su."

Wata majiya ta kuma ce an gano wata tattaunawa da Idirisa ke yi ne da wata kungiyar jin kan mutane kuma aka gano yana neman ayi sulhu.

Majiyar ta ce kashe Idirisa ya kara rura wutar rikicin da ke kungiyar ta Boko Haram inda wasu daga cikin masu masa biyaya su kayi barazanar yin bore.

Wasu daga cikin mayakan sun zargi shugabanninsu da rudar su.

Wannan na zuwa ne a lokacin da kungiyar ta rasa kwamandojin ta kimanin su 25. Sojojin Najeriya sun kai hare-hare da dama a sansanin na 'yan Boko Haram.

Majiyar ta ce wasu da dama sun tsere zuwa kasashen Chadi, Nijar da Kamaru sakamakon luguden wutan da sojojin ke musu.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa wani Abba Gana ne sabon shugaban na kungiyar ISWAP ta Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164