Hukumar NECO ta sallami ma’aikata 19 masu amfani da takardun karatu na bogi

Hukumar NECO ta sallami ma’aikata 19 masu amfani da takardun karatu na bogi

Kwamitin gudanarwa ta hukumar shirya jarabawar kammala karatun sakandari a Najeriya, NECO ta amince da fatattakar wasu ma’aikatan hukumar 19 da aka samu suna amfani da takardun karatu na bogi.

Daily Trust ta ruwaito shugaban sashin watsa labaru da hulda da jama’a na hukumar, Azeez Sani ne ya bayyana haka inda yace kwamitin tantance ma’aikata da hukumar ta kafa ne ta bankado wadannan mutane.

KU KARANTA: PDP ta bukaci kotun koli ta sake nazari game da hukuncin shari’ar zaben shugaban kasa na 2019

Sani ya ce yadda aikin kwamitin ya gudana shi ne ta gayyaci wasu ma’aikatan hukumar da ake zarginsu da amfani da shaidun kammala karatu na bogi, inda suka amsa tambayoyi daga wajenta, kuma a nan ne suka tabbatar da rashin ingancin takardunsu.

“Haka zalika kwamitin ta fadada bincikenta har zuwa wajen hukumar inda ta tuntubi makarantu da cibiyoyin ilimi da mutanen suka yi ikirarin halarta a baya, inda dukkanin makarantun da cibiyoyin suka musanta saninsu.” Inji shi.

Ya kara da cewa a zaman kwamitin gudanarwar hukumar NECO na 52 ne aka gudanar da nazari a kan rahoton tantance ma’aikatan, inda kwamitin ta bayyana amincewarta da rahoton, sa’annan ta umarci a sallami ma’aikatan da binciken ya shafa.

Ko a zaman kwamitin na musamman na 17 da ta gudanar a watan Nuwambar shekarar 2019 ta amince da sallamar ma’aikatan hukumar 70 da ka kama da laifin amfani da takardun karatu na bogi, amma Sani yace aikin tantancewar na cigaba.

A wani labari kuma, a sakamakon rikicin kabilanci tsakanin makiyaya da manoma wanda ya sabbaba samun hare haren yan bindiga a wasu yankunan kudancin Najeriya, wata kabila dake jahar Delta ta haramta ciniki da cin naman shanu a tsakanin jama’anta.

Jaridar Punch ta ruwaito kabilar Uwheru dake karamar hukumar Ughelli ta Arewa ce ta dauki wannan tsatstsauran mataki, inda tace ba’a kara sayar da naman shanu ko cin naman shanu a masarautarta don nuna bacin ranta ga hare haren da ta ce makiyaya suna kai ma manomanta da sauran jama’a.

Wannan sabuwar doka da shuwagabannin al’ummar kabilar Uwheru suka kirkiro ya biyo bayan wasu hare hare da suke zargin makiyaya ne suka kai masarautar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: