Allah ya yi wa tsohon kocin Kano Pillars, Kabiru Baleria rasuwa

Allah ya yi wa tsohon kocin Kano Pillars, Kabiru Baleria rasuwa

- Kabiru Baleria tsohon kocin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ya rasu

- Baleria ne mataimakin Emmanuel Amunike a tawagar 'yan kwallon Najeriya na kasa na kasa ta shekaru 20 a 2016

- Tsohon dan wasan ya yi fama da matsalar matsanancin damuwa kafin rasuwarsa a Kano

Tsohon mataimakin kocin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Kabiru Baleria ya rasu.

Kabiru Baleria ya yi fama da matsalar matsananciyar damuwa na wasu watanni kuma ya tafi asibitoci da dama an masa magani a Kano kafin daga bisani ya rasu a yammacin ranar Talata 25 ga watan Fabrairu.

Kamar yadda binciken da Legit.ng ta yi ya nuna bayan rasuwarsa, Kabiru Baleria ya kamu da rashin lafiya ne bayan da matarsa ta tsere Amurka da 'ya'yansu uku.

Matarsa ta kira ta ce ya manta da batunta da yaranta a lokacin da ta isa Amurka kuma hakan ne ya yi sanadiyar Kabiru Baleria ya kamu da hawan jini.

Manyan shugabanni na hukumar kwallon kwafa ta Najeriya sun yi kokarin lalashin matar Kabiru Baleria ta dawo Kano tare da yaransa amma hakan bai yi wu ba.

Kabiru Baleria ya fara wasan kwallo ne a Kano Pillars inda ya buga kakkan wasanni biyar sannan ya tafi Elkanemi Warriors a Borno amma daga baya ya sake dawowa Kano Pillars.

DUBA WANNAN: Kwankwaso ya jahilci yadda kotu ke aikin ta - Kwamishinan Ganduje

Baleria bai samu yadda ya ke so ba a matsayinsa na dan kwallo hakan yasa ya dena wasa ya tafi ya yi karatun zama koci sannan ya dawo Kano Pillar a matsayin manajan kungiya.

Yana matsayin manajan tawagar ne lokacin da tsohon koci Mohammed Baba Ganaru ya lashe kofin Firimiya ta Najeriya sau biyu a jere. Kabiru kuma ya yi aiki karkashin Kadiri Ikhana da Okey Emordi.

A Janairun 2019 ne aka nada Kabiru Baleria matsayin koci na wucin gadi kuma wasarsa na farko ya yi nasara 2-0 a kan ElKanemi Warriors.

A halin yanzu Kano Pillars ne ke na 10 a teburin Firimiya na Najeriya da a yanzu an buga wasanni 20.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel