Yanzu-yanzu: Ganduje ya haramta wa Almajirai bara a titunan Kano

Yanzu-yanzu: Ganduje ya haramta wa Almajirai bara a titunan Kano

A kokarin tabbatar da ilimin firamare da sakandare kyauta a jihar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya haramta wa almajirai bara a titunan jihar.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin kaddamar da shirin ilimin farko ga kowa (BESDA) tare da raba shaidar daukar aiki ga malami 7,500 a jihar.

Wannan na kunshe ne a takardar da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Abba Anwar ya fitar.

Kamar yadda gwamnan ya sanar, hada tsarin karatun almajiran da sabon tsarin zai tabbatar da toshe barakar bara a jihar gaba daya.

Ganduje ya ce: “Wannan tsarin na ilimi kyauta kuma na dole ga ‘yan firamare da sakandare zai taka rawar gani wajne gyan tsarin iilimin almajirai na jihar. Za a dinga koya musu turanci da lissafi duk a cikin tsarin makarantun almajiran.”

Yanzu-yanzu: Ganduje ya haramta wa Almajirai bara a titunan Kano
Yanzu-yanzu: Ganduje ya haramta wa Almajirai bara a titunan Kano
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kwankwaso ya jahilci yadda kotu ke aikin ta - Kwamishinan Ganduje

“Yayin da almajiran zasu ci gaba da koyon karatun Qur’ani, za su dinga koyon turanci da lissafi da zai basu damar karatun sakandare da gaba da ita a saukake,” ya bayyana.

Gwamnan ya ce an diba malamai sabbi 7,500 wadanda za a raba su zuwa Islamiyyu da makarantun almajirai na jihar ta yadda za a hade tsarin karatun.

Ganduje ya kara da jan kunnen malaman wadanda zasu iya jayayya da sabon tsarin. Ya jaddada cewa, “idan kana tunanin ba za ka iya karbar sabon tsarin ba, toh ka bar jihar.”

Hakazalika, ministan ilimi Adamu Adamu, ya jinjinawa kokarin gwamnatin jihar Kano din a fannin ilimi. Ya ce jihar ta dauka sabon tsarin da zai kasance abin koyi ga sauran jihohin.

Adamu ya samu wakilcin darakta daga ma’aikatar ilimi, Mrs Liman

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164