Lauyan Olisa Metuh ya yi martani kan hukuncin da aka yanke wa wanda yake karewa

Lauyan Olisa Metuh ya yi martani kan hukuncin da aka yanke wa wanda yake karewa

Abel Ozioko, lauyan Olisa Metuh, ya ce a shirye yake don daukaka karar hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Abujan ta yankewa wanda yake karewa na shekaru 39 a gidan gyaran hali.

Okon Abang, alkalin kotun ya sakankance cewa tsohon kakakin jam’'iyyar PDP din ya aikata laifuka bakwai da ake zargin sa da su na almundahanar kudade, kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

A laifi na farko da na biyu, Metuh ya samu hukuncin shekaru bakwai a gidan gyaran hali. Laifi na uku kuwa ya samar masa da shekaru biyar a gidan gyaran halin. Laifin na hudu ya samu shekaru bakwai sai laifi na biyar da na shida sun samar masa da shekaru uku-uku a gidan yari. A laifi na bakwai ne yake da shekaru bakwai a gidan gyaran halin.

Kamar yadda alkalin ya bayyana, dukkan shekarun za su tafi ne tare. Ma’ana kuwa Metuh zai kwashe shekaru bakwai a gidan gyaran hali.

Lauyan Olisa Meetuh ya yi martani kan hukuncin da aka yankewa wanda yake karewa
Lauyan Olisa Meetuh ya yi martani kan hukuncin da aka yankewa wanda yake karewa
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Kotu ta aike wa shugaban gidan yari sammaci a kan hana El-Zakzaky ganin likita

A yayin kwatance, lauyan Metuh ya kwatanta hukuncin da “mummunan hukunci”. Ozoko ya zargi alkalin da yin gwaji da wanda yake karewa.

“Muna da damar dauakka kara. Ina da kwarin guiwar cewa zamu yi nasara a kotun gaba. Zamu tunkari mutane uku don gane cewa muna da gaskiya ko babu,” ya ce.

Metuh wanda yayi shiga cikin sutura mai launin bula ya iso ne tare da sandar guragu. ‘Yan uwansa mata biyu tare da sauran iyalansa duk sun hallara a kotun.

Bai nuna tashin hankali ba amma sai murmushin da aka gan shi yana yi yayin da aka dauke shi a mota mai launin kore don mika shi gidan gyaran halin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel