Abin mamaki: An kama mace mai garkuwa da mutane a Niger

Abin mamaki: An kama mace mai garkuwa da mutane a Niger

Yan sandan jihar Niger sun kama wata mata mai shekaru 32, Hassana Bala da ke zaune a Usuba a Kontagora a jihar Niger bayan ta yi yunkurin garkuwa da wani Umar Sarkin Turaku da ke kauyen Kawo a karamar hukumar Kontagora na jihar.

Bincike da aka gudanar ya nuna cewa matar mai 'ya'ya biyu da rabu da mijinta kafin ta shiga sana'ar na garkuwa da mutane kafin daga baya 'yan sandan 'B' Division Kontagora suka kama ta bayan wani ya tsegunta musu.

The New Telegraph ta gano cewa wacce ake zargin ta yi shirin sace wani a ranar Laraba 19 ga watan Fabrairun 2020 amma aka kama ta bayan Turaku ya sanar da 'yan sanda cewa ana masa barazanar sace shi.

Rahotanni ya nuna cewa Hassana Bala ta dade tana yi wa wanda aka so a sace (Turaku) barazana kuma ta ce za ta sace shi idan bai biya ta Naira miliyan 50 ba.

Abin mamaki: 'Yan sanda sun damke mace mai garkuwa da mutane a Niger
Abin mamaki: 'Yan sanda sun damke mace mai garkuwa da mutane a Niger
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Ganduje ya haramta wa Almajirai bara a Kano

Da ta ke amsa tambayoyin manema labarai, ta shaidawa majiyar Legit.ng cewa sabon masoyinta ne ya koya mata garkuwa da mutane, ta kara da cewa mutane ba su san tana garkuwa da mutane ba.

A cewarta, "Bayan na rabu da miji na, na hadu da wani aboki na miji da ya nuna min harkar kuma ta hakan ne na fara salwantar da rayuwa ta saboda kudi. Abinda na aikata zubar da mutuncin mata ne.

"Tunda muka rabu da miji na, rayuwa ta ta tabarbare; Duk abinda na aikata rikici ya ke zama. Rayuwa kwata-kwata ba ta min dadi. Abin takaici ne wannan.

"Na yi nadamar abinda na aikata; 'yan uwa na, 'ya'ya da kawaye na duk za su guje ni amma ina addu'an Allah ya sanyaya zuciyarsu su yafe min."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel