Tirkashi: Bazawara ta tonawa wani magidanci da ya nemi lalata da ita asiri

Tirkashi: Bazawara ta tonawa wani magidanci da ya nemi lalata da ita asiri

- Wata mata mai takaba ta ci zarafin wani mutum da ya kirata tsirara ta facebook

- Ta bayyana cewa mutumin ya dade yana bibiyarta amma sai ya kirata yayin da take wajen biki kuma tsirara

- Bayan nuna mishi rashin jin dadinta, sai kawai ya fara zaginta tare da kiranta karuwa mai kwana da maza kala-kala

Wata mata mai takaba mai suna Obong-anwan ta yi kira ga maza masu aure da ke kokarin makale mata a kan su kiyayeta, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Kamar yadda Obong-anwan ta sanar, wani mutum mai suna Samuel Usoro yana ta bibiyarta don neman soyayyarta.

Matar ta ce mutumin ya kira ta amma lokacin tana wajen biki. Saboda kin daukar da tayi ne ya zazzageta. Ta ce ba wai ta yi wallafar bane don tozarta shi, sai don zaginta da yayi.

Tirkashi: Bazawara ta tonawa wani magidanci da ya nemi lalata da ita asiri
Tirkashi: Bazawara ta tonawa wani magidanci da ya nemi lalata da ita asiri
Asali: Facebook

Obong-anwan ta rubuta;

Gareka Samuel Usoro, na ziyarci bayananka a faceebook amma na gane kai karamin yaro ne da ke iya fusata a kan kananan abubuwa duk da kuwa kai mijin wata ne.

Shawarar da ka bani na cewa in yi aure saboda ina tsufa, abin kunya ne a gareka. Babu dadewa zaka mutu kuma matarka za ta zama uwar marayu yayin da wasu zasu tsangwameta.

KU KARANTA: Harin Garkida: Muna kallon jiragen sojin saman Najeriya a kan mu lokacin da 'yan Boko Haram suka kawo mana hari

Ta yaya muka kai haka da kai?

Naje biki ne kuma ina tare da kawayena kawai sai gani nayi wani mutum tsirara na kirana a waya. Sai na gane wani mutum ne da ya dinga yi min magana ta facebook amma yau sai ya kira ni. Ban san yadda aka yi na dau wayar ba amma an ci minti uku. Daga nan sai na tura mishi sakon rashin jin dadin abinda yayi min.

Daga nan kuwa sai ya fara zagina. Ban taba yin irin wannan cin mutuncin ga kowa ba. Yana kirana karuwa mai kwana da maza kala-kala. Wannan mutumin bai san komai a kaina ba.

Bai san har ‘ya’ya gareni ba kuma mutuwa mijina yayi ba. Yana gani na a matsayin budurwa wacce ta kosa tayi aure. Ban ci zarafin shi don komai ba sai don zagin da yayi min.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel