Mataimakin Ministan Lafiya na Iran ya kamu da Coronavirus

Mataimakin Ministan Lafiya na Iran ya kamu da Coronavirus

Mataimakin ministan na kasar Iran ya kamu da kwayar cutar Corona wacce bullar ta ya kashe mutane 15 a kasar.

Babban jami'in lafiyar, Iraj Harirchi, a wata hirar da aka yi da shi ta bidiyo na shafin Intanet ya ce ya kebe kansa kuma ya fara shan magunguna.

An hange shi yana da goge girarsa a yayin taron manema labarai a ranar Litinin inda ya musanta cewa mahukunta a kasar suna karya kan adadin yaduwar cutar da Convi-19.

A ranar Talata wani dan majalisa daga babban birnin kasar Tehran, Mahmoud Sadeghi shima an ce ya kamu ta kwayar cutar ta Convid-19.

Mataimakin Ministan Lafiyan Iran ya kamu da Coronavirus
Mataimakin Ministan Lafiyan Iran ya kamu da Coronavirus
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kaduna: Kotu ta aike wa shugaban gidan gyaran hali sammaci kan hali El-Zakzaky ganin likita

Mataimakin ministan lafiyar dan shekara 57 ya rubuta a Twitter, "Na cire tsammani da cigaba da rayuwa a duniyan nan."

Iran ta ce mutane 95 ne suka kamu da kwayar cutar a kasar amma ana tunanin adadin ya fi hakan.

Direkta Janar na Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ya ce karuwar yaduwar cutar ta Corona abin tayar da hankali.

Baya ga kasar China ta cutar ta bulla, kasar Iran ita ce kasa da mutane suka fi mutuwa.

A kalla mutane 80,000 suka kamu da cutar a dimiya tun bullar ta a shekarar 2019. Kimanin mutane 2,700 sun mutu.

Bullar cutar a Iran ya tayar da hankulan mutane duba da cewa miliyoyin mutane suna ziyartar kasar domin Ibada a duk shekara. Ana tsoron daga Iran cutar tana iya yaduwa zuwa sauran kasashen gabas ta tsakiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel