Rikicin makiyaya da manoma: Wata kabilar kudancin Najeriya ta haramta cin naman shanu

Rikicin makiyaya da manoma: Wata kabilar kudancin Najeriya ta haramta cin naman shanu

A sakamakon rikicin kabilanci tsakanin makiyaya da manoma wanda ya sabbaba samun hare haren yan bindiga a wasu yankunan kudancin Najeriya, wata kabila dake jahar Delta ta haramta ciniki da cin naman shanu a tsakanin jama’anta.

Jaridar Punch ta ruwaito kabilar Uwheru dake karamar hukumar Ughelli ta Arewa ce ta dauki wannan tsatstsauran mataki, inda tace ba’a kara sayar da naman shanu ko cin naman shanu a masarautarta don nuna bacin ranta ga hare haren da ta ce makiyaya suna kai ma manomanta da sauran jama’a.

KU KARANTA: PDP ta bukaci kotun koli ta sake nazari game da hukuncin shari’ar zaben shugaban kasa na 2019

Wannan sabuwar doka da shuwagabannin al’ummar kabilar Uwheru suka kirkiro ya biyo bayan wasu hare hare da suke zargin makiyaya ne suka kai masarautar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10.

Majiyarmu ta ruwaito kabilar Uwheru na daga cikin masarautu 24 dake cikin yankin Urhobo a jahar Delta, inda ta kara da cewa a ranar Asabar 22 ga watan Feburairu ne masarautar ta yanke hukuncin a wani taro da ya samu halartar manyan yayan masarautar.

Daga cikin wadanda suka halarci taron har da Farfesa Patrick Muoboghare, kwamishinan ilimin gaba da sakandari a gwmanatin jahar Delta, kuma mahalarta taron sun zartar da cewa dokar ta fara aiki ne nan take.

Wata majiya ta bayyana cewa: “Da wannan doka, babu wanda zai kara kawo nama a cikin masarautar Uwheru a kowanne irin taro, ko mutuwa ko biki, babu yadda za’a yi kuna kashemu kuma kuna so mu ci naman shanu a lokacin da jama’anu ba su iya zuwa gona.” Inji shi.

A wani labarin kuma, shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jahar Oyo, Alhaji Yakubu Bello ya yi kira da a saka yan Fulani a cikin kungiyar tsaro ta musamman da gwamnatocin jahohin yarbawa ta kirkiro don kare yankin mai suna Amotekun.

Kamfanin dillancin labarun Najeriya, NAN, ta ruwaito Bello ya bayyana haka ne yayin taron sauraron ra’ayoyin jama’a game da kudurin dokar kafa rundunar Amotekun daya gudana a majalisar dokokin jahar Oyo a ranar Litinin.

A jawabinsa, Bello ya ce ba dukkanin bafulatani bane mutumin banza, kuma mutumin banza ne kadai yake tsoron kafa sabuwar hukumar tsaro, shi yasa ya bukaci a sanya Fulani a rundunar, don haka ya bayyana goyon bayansa ga yunkurin kafa rundunar Amotekun.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel